April 16, 2024

Apply For 2022 Nigerian Police Force Recruitment

Barkanku da zuwa wannan site namu mai suna Hausatiktok. Com.Ng

Hukumar Aikin Dan Sanda wato ‘Nigerian Police’ tana sanar da al’umma cewa ta bude shafinta domin diban sabbin ma’aikata a yau Litinin 15th ga watan August, 2022.

Hukumar ta ‘yan sanda tana sanar da duk mai sha’awar yin aikin Dan Sanda wato wanda yake son yin aiki a karkashin wannan hukuma ta Nigerian Police da ya garzaya shafinta domin yin rijista.

Hukumar za ta dauki ma’aikatan ne da matakin ‘Police Constable’

ABUBUWAN DA SUKE BUKATA

Hukumar ta ‘yan sanda tana bukatar mai sha’awar aikin ya ciki wadannan sharadai:

  • Dole ne wanda zai cike aikin ya zama dan Nijeriya.
    Dole ne wanda zai cike aikin ya kasance ya mallaki katin zama dan kasa (Notional I’d Card)
  • Dole ne wanda zai cike aikin ya kasance yana da lambar waya da kuma Email Address.
  • Dole ne wanda zai cike aikin ya kai shekara 18, sannan kuma kar ya haura shekara 25.
  • Dole ne wanda zai cike aikin ya zama ya kammala karatun Sekandare ( Secondary School )
  • Dole ne wanda zai cike aikin ya zamana ya yi pass na a kalla 5 credit; cikin biyar din kuma ya kasance da English da Mathematics.
  • Dole ne wanda zai cike aikin tsayinsa ya kai 1.67M, mace kuma tsayinta ya kai 1.64M.

YADDA ZA KA YI APPLY.

Da farko za ka shiga shiga site dinsu ‘ http://www.recruitment.psc.gov.ng

Bayan ka shiga zai nuna ma inda aka rubuta ‘apply’ sai ka shiga, idan ya bude za ka ga inda zaka sa email da password daga kasa za ka ga inda aka rubuta signout/register sai ka shiga ka yi register.

Za su tura maka sako ta email dinka sai ka je cikin email dinka ka yi confirm, sannan ka karasa cikewa abubuwan da za su bukaci ka sa musu.

Allah Ya taimaka, Ya ba wa kowa sa’a.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *