June 9, 2024

IKON ALLAH SAI KALLO WATA MATA TA HAIFI ‘YA’YA 19 A RANA DAYA KUMA DUK SUNA CIKIN KOSHIN LAFIYA TIRKASHI

Ikon allah sai kallo wata Mata mai suna Halima Cisse mai shekaru 25 yar asalin kasar Mali ta haife jarirai tara a rana guda wanda lamarin ya firgita likitoci da masu karbar haihuwar ta. 

Gwamnatin kasar Mali itace ta dauki nauyin Halima inda aka tura ta kasar Maroko domin kulawa daga wajen kwararrun likitoci wanda mijinta ya nuna farin cikinsa a wata tattaunawa da yai da BBC. 

Yace matarsa ta haifi yara tara maza hudu mata 5, kuma dukkan su suna cikin koshin lafiya, a cewar sa. Sannan ya mika godiyarsa ga al’umma daga sassan duniya da suka taya shi murna da kyautar da Allah ya basu. 


Rabon da a samu wata mace da ta haifi jarirai da yawa tun a shekarar 2009 inda wata ‘yar kasar Amurka ta haifi jarirai takwas, wanda hakan yasa ta karbi kambun duniya na wacce ta haife jarirai da yawa cikin koshin lafiya. 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *