May 22, 2024

Baxa Kuyi Asarar Kudadden Ku Ba’ Idan Allah Ya Sa Nazama Sabon Shugaban kasar” Nigeria” Kwankwaso

CANJIN KUƊI: Dan takarar shugaban kasar Nigeria a karkashin jam’iyar Nnpp kuma tsohon gwamnan jahar kano’ Dr Rabiu musa kwankwso. Ya jajintawa Yan nigeria akan Wa’adin Dena Karbar Tsoffin takardun Kudadde.

Kwankwso yayi kira ga ƴan Nigeria suyi haƙuri subi layi su canja kuɗin da suke dashi, tunda Gwamnati taƙi tausaya musu, sannan ranar zaɓe subi layi don canja waɗannan bara gurbin shugabannin.

Kwankwso ya Kara da cewa Nidai ina tabbatar muku, duk wanda bai samu ya canja kuɗin sa ba, muddin na zama shugaban ƙasa bazan taɓa bari yayi asarar kuɗinsa ba.

Zan tabbatar kowa ya canja kuɗin sa, ba tare da yayi asarar ko sisi ba, domin bazai yiwu ka tara haƙƙin ka da wahala wani yazo yace shikenan ya tashi a banza ba.

Duk da jam’iyar Nnpp ta kasance Sabuwar jam’iya ama Batun kwankwso ya Kara wa jam’iyar farin jini a idon Yan Nigeria.

A cewar sa Baxai gaxaba zai Tabbatar babu wanda yayi asara Kudadde Idan ya Zama shugaban kasa kowa zai kashe Kudin sa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *