May 18, 2024

Innalillahi: Tafiyar kilomita 27 ne tsakanin ƙauyen da ake kira Illela da asibiti mafi kusa a garin Gashua na jihar Yobe, da ke arewacin Najeriya.

Amma ba nisan ne babbar matsalar ba, rashin kyawun hanya ne abin da ya fi ci wa al’ummar kauyen tuwo a kwarya.

A lokacin damina Illela kan koma tsibiri, inda ruwa kan zagaye shi, ta yadda ba a iya shiga ko fita sai ta hanyar amfani da kwale-kwale, kuma wannan babban ƙalubale ne musamman a lokacin da aka samu maras lafiya, ciki har da mata masu haihuwa.

A nan ne kauyen da Shafi’u Salisu ke rayuwa tare da matarsa da yara biyu.

Duk da cewa Shafiu ya yi sa’a, yaransa biyu, Zainab da Fatima an haife su ne lokacin rani, dan’uwansa bai yi wannan dacen ba.

Ya ce “lokacin da Hajara, matar yayana za ta haihu, sai muka nemi amalanke muka saka ta a ciki zuwa bakin rafi, daga nan sai muka saka ta a kwale-kwale muka tsallakar da ita kafin muka nemo motar da ta kai ta asibiti.”

Shafi’u ya bayyana haka ne a yayin wata hira da BBC a shirin da muke yi na musamman game da abubuwan da suka shafi rayuwar jama’a gabanin zaɓen Najeriya na 2023.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *