May 27, 2024

Amal Umar ta gurfana a gaban kotu bayan ta ci kudin wani Saurayi miliyan 7 ita da mahaifin ta.

Fitacciyar jarumar Kannywood Amal umar ta gurfana a gaban kotu bayan An kama wani Saurayinta da ake zargin ya cinye kudi kimanin miliyan 40.

Tun da fari dai Amal nada wani Sauri mai suna Ramadan Wanda wani mai gidan sa ya bashi kudi Naira miliyan 40 da sunan za ai kasuwanci da ita ya salwantar da kudin gaba data.

Saurin ya gurfana a gaban kotu bisa zargin sa da lashe makudan kudaden, Inda ya bayyanawa Al’kali cewa budurwar sa Jaruma Kannywood Amal ya budewa da naira miliyan 5 ya kuma bawa mahaifin jarumar miliyan 3 domin ya kashe sabgar gaban sa

A zaman kotun da akai a jiya Alhamis An kamon jaruma Amal inda aka sakayeta Aka kuma karbe Motar da saurin ya siya mata.

Bayan ta samu beli, daga baya sai Amal ta shigar da ƙara ta hannun lauyar ta, Adama Usman, a kan ta na neman kotun ta hana jami’an ‘yan sanda su kama ta har zuwa ranar da za a koma kotun, wato abin da ake kira ‘injunction’.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *