April 20, 2024

Hukumar Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kaduna Ta Yi Nasarar Damke Wasu Informers ‘Yan Mata 2 Da Makamai Na AK AK a cikin buhu za su kai ma ‘Yan Bindiga a Jihar Kaduna.

Kalli Bidiyon:

https://youtu.be/1qf0mbFRTrE

Kamar yadda kuka kalla a bidiyon dake sama, Ita dai Fatima ta cr bata san ko menene ba cikin Buhunan da suke dauka suke kaiwa daji sai daga baya.

Hakazalika ta kara da cewar ita fa tana raka kawarta ne kawai, hasalima sau daya ne tak ta taba daukan buhun da suka sauka a kan mashin ta dafa mata kafin ta karbi abinta.

Ta ce buhun dai yana da nauyi kuma yana da tsawo, da ta tambayeta ta nuna mata abinda ke buhun sai tace ba sai ta nuna mata ba amma dai bindigogi ne a ciki in ji ta.

Ita kuwa Ràbi tace an taba kamata a baya har aka mika ta ga rundunat yan sanda, su kuma suka yi bincike kana suka mika ta ga kotu, amma dai an bi wata hanya an sake ta kuma an yafe mata.

Duk da cewar hakan bai sanya ta bar safarar makaman ba, amma dai ta ce yayanta take kai mawa, kuma wani abokinsa yayi mata alkawarin aure shine dalili.

Kun ma ji yadda janzakitv ta kawo maku labarin yadda yan sanda a jihar bauci suka kama wasu yan banga biyu da bindigogin toka suka yi ma wata matar aure fyade.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *