June 20, 2024

Ya shige cikin daki shi kadai don gani. Wannan abu bai yiwa angon dadi ba kuma take ya yanke shawarar kawo karshen shagalin da ake yi. Kai tsaye Angon ta danna mata saki. Daga baya Amaryar ta bayyana cewa lallai sun yi soyayya da tsohon saurayin amma daga baya suka fahimci cewa basu dace da juna ba. Sai ta yanke shawarar watsi da shi tunda iyayenta sun sama mata sabon saurayin da ya dace da ita. Tsohon Saurayin ya bukaci ta ziyarcesa ana gab da aure Ta kara da cewa tsohon saurayin ya bukaci ta kawo ziyara gidansa ana sauran yan kwanaki da aure amma tayi banza da shi. Ta ce ba ta son ta sake maimaita irin kura-kuran da tayi a baya saboda tana son fara sabuwar rayuwa da mijinta. Ashe wannan abu bai yiwa tsohon saurayin dadi ba inda ya fara dura mata ashariya kuma yayi alkawarin tona mata asiri.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *