May 27, 2024

Innalillahi duniya tazo karshe kalli Irin iskanci da suke a idon jama’a ko kunya babu.
Abinda Iyayen Yanzu suka dauka Jin Dadin Aure shi ne. Namiji ya dinga Kashewa Diyarsu Kudi Kafin ya aureta da Bayan ya aureta. Wannan a wajensu shi ne so. Kuma Shi ne Jin Dadin Aure.

Hakan yasa Su ma matan da yawa suka tafi akan wannan Tsarin.

Su Kuma Maza sai suke amfani da wannan damar Wajen Cuta da Gallazawa Matan sbd ganin abin hannunsu sukeso ba ainahin su Kansu ba a zallar Asalin Dan’adamtaka.

Ada Surukai kamar Iyaye ne ana girmamasu kamar yadda ake girmama iyaye. Amma yanzu da Kwadayi ya bayyana da Kuma kowa na son nasa. Sai abubuwa suka Canja.

Allah ya datar damu. Yasa a dinga Soyayya don Allah. A Kuma girmama Juna Don Allah.

Duk Wanda zai Gina rayuwar aurensa ya nemi daidai shi kar ya biyewa son zuciyarsa daga Karshe shi ne ake yin Nadama.

Gidan aure ya zama Babu zaman lafiya da Kwanciyar hankali. Kullum ana cikin Korafi da Kai Kuka ga Iyaye da Kuma kafofin Sada Zumunta ana (Hide my ID).

Ada Matsalolin mutane ana gabatar dasu ne ga Malaman addini su maka addua ko su baka adduar kayi da kanka. Amma yanzu an dawo da ita Social Media.

Ada mata basa Sakaci da addua akan Matsalolinsu na zamantakewar aure. Amma yanzu sun yi Sakaci sun bar addu’ar sun dawo da komai nasu Social media.

Zan cigaba da Zakulo muku wasu Matsalolin musamman wadanda suka Shafi zamantakewar Aure da yadda za a Gyara. In da hali ma a dinga fadin addu’o’in da mutum zai yi da Kansa ba sai yaje Wajen boka ko Malam ba. Ko yakawo mana korafinsa Nan Social media ba.

daga uncle larabi,

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *