May 18, 2024

Innalillahi R.I.P Abokan Karatun Sane Sukai Masa Sukan Tsiya Har Saida Ya Mùtu

INNA LÍLLAHÍ WA’INNA ILAIHÍ RAJI’ÚN

Wasú Dalibaí Sún Yi Sanadíyar Mútúwar Abokín Karatúnsú A Makarantar Lafíya Daké Jìhar Sókótó

DÁGA Real Buroshi Mawaka Sókótó

Wasu ɗalibai a makarantar kiwon lafiya ta Sultan Abdurrahman School of Health Technology Gwadabawa dake jihar Sokoto, sun kashe abokin karatun su har lahira ta hanyar yi masa bugun kawo wuƙa har ya zamo sanadiyar mutuwarsa a daren jiya Lahadi.

Ɗalibin mai suna Lukman wanda aka fi sani da Khalifa ɗan garin Kalambaina mai karatu a sashen lafiyar haƙori (Dental& surgery department) aji na biyu (200L) ya rasa ransa ne a sanadiyar wani zargin da abokan kwanansa ke yi mishi wanda ba su da tabbacin hakan, bayan cece kucen da ya faru a tsakanin shi margayin da abokan nasa ne har yakai suka yimasa taron dangi suka zamo sanadiyar rasa rayuwarsa.

Wannan mummunan lamarin ya faru ne a wajen makaranta cikin gidajen hayar kwanan su, inda yanzu haka hukuma na kan ƙwakkwaran bincike game da lamarin.

Kyakkyawan Hadisi Daga Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam)ya ce: ‘Idan mutum ya mutu danginsa suka shagaltu da jana’izar sa,wani kyakkyawan mutum zai tsaya a kansa a Lokacin da ake rufe jikin mamaci, wannan mutumin yakan shiga tsakanin mayafin da kirjin mamacin. Lokacin da aka gama binne sa, mutane suka dawo gida, mala’iku 2, Munkar da Nakeer (Mala’iku biyu na musamman masu tambayar kabari), zasu zo cikin kabarin sa suna kokarin raba wannan kyakkyawan mutumin da mutumin da ya mutu, don su sami damar yi wa mamacin tambayoyi a game da imaninsa. Amma kyakkyawan mutumin nan zai ce, ‘Abokina ne shi. Ba zan barshi shi kadai ba. Idan an nada ku don yin tambayoyi, kuyi aikinku. Ba zan iya barin shi ba sai na shigar da shi Aljannah ‘. Bayan haka sai ya juya ga abokinsa (mamacin nan) ya ce, ‘Ni ne Alkur’ani, wanda ka saba karantawa, wani lokacin da babbar murya wani lokaci kuma da karamar murya. Karka damu. Bayan Munkar da Naker sun game maka tambayoyi, ba za ka sami baƙin ciki ba. ‘

Lokacin da Munkar da Nakir suka ƙare tambayoyin su ga wannan mamacin, sai kyakkyawan mutumin nan ya shirya masa daga Al-Mala’ul A’laa, shimfiɗar siliki cike da miski

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *