May 18, 2024

Innalillahi Wainna ilaihirrajiun Kwana Biyu da Auren su Ya rasu Allah Ya gafarta Masa.

Wani Matashi Kenan wanda Allah ya Karbi Rayuwar shi kwana biyu dayin aurenshi. Tasiu Adam Abdullahi Wani dan uwa ne ga Mamacin shine ya wallafa a shafinsa kamar haka.

Mutumin kirki ne me san jama a,daurin auren sa shekaran jiya asabar ya isa ka tabbatar da haka,jiya da magriba na ganshi da dan sa yake mana Godiya da ban gajiya amma yanzu mun yi bankwana dashi ya sadu da mahaliccin sa yan uwa, masoya makusanta da iyalan sa ga sabuwar amarya da tarewa ba aiba duk bai hana Allah gayyatar sa ba ya Allah ka gafarta masa kusakuran sa kasa aljanna makoma


1.ba abin da ke hana ajali zuwa
2.tayiwa cikan buri yana tare da ajali
3.kayi wa mutuwa tanadi dan bata sanrwa
4.arzikin ka da jama’arka baza su hana ka mutuwa ba kada manta lahira
5.ka zauna da kowa lafiya baka san lokacin mutuwa ba
6.mutwa wa’azi ce,amma jinsin wadanda a kai wa tafi duka matasa su kudi ku gina lahira ba gasar gidaje shaguna da plotai ba in ka mutu sai da a kirga su kawai amma ba za ka tafi da komai ba
A karshe muna addu ar Allah ya gafarta masa da sauran musulmi baki daya

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *