June 11, 2024

Innalillahi wa’Inna’ilaihi raji’un wasu mutane daba asan ko suwaye ba’ sun shiga gidan wata baiwar allah a jihar taraba domin ganin sun sakata a cikin damuwa.

An Shiga Har Gidan wata baiwar Allah anyiwa Jariran ta ‘Yan Biyu Yankan Rago A Jihar Taraba state dake Nigeria, subahanallahi.

Lamarin ya faru ne a Unguwar Dossa Zing dake jihar Taraba, Inda aka shigo har cikin daki aka samu yara jarirai kuma ‘yan biyu aka yi musu yankan rago.

Daga Alhaji Maiwada Atake Jalingo dake jihar taraba dake Nigeria, yayin da yake zantawa da manema labaran gidan jaridar Vanguard News, ya bayyana cewa.

Lamarin ya faru ne a safiyar ranar lahadi data 17/07/2022, da misalin karfe shida na safe yace’ mahaifiyar yaran ta waye gari dasu cikin koshin lafiya.

Har tayi musu wanka da kuma kwalliya ta musamman kafin daga bisani ta kewaya izuwa bayin domin ganin ta gyara jikin nata itama, ta hanyar yiwa kanta wanka da kuma kwalliya a lokacin.

Fitowar ta keda wuya daga toilet din ta sai kuwa ta riski ganin wannan mummunan lamarin daya faru da jariran, nata a lokacin kafin kace miye matar ta yanke jiki ta fadi saboda ganin abinda ya faru da ‘ya’yan nata.

Yanzu haka dai Jami’an tsaron jihar Taraba sun baza komar su, wurin ganin sun tabbar da kamo duk wanda suke da hannu cikin wannan lamari daya faru a jihar ta Taraba.

Kuci gaba da Kara kasancewa da shafin mu mai albarka Janzakitv, domin samun labaran mu kowace Rana da zarar mun samu Mungode.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *