May 23, 2024

Innalillahi wa’Inna’ilaihi raji’un wasu ‘yan Bindiga Sun Kashe Iyalan Sarki Su Bakwai A Jihar Taraba Bayan Sunyi Garkuwa Da Su a daren jiya a yankin jihar ta taraba state.

Mai Martaba Sarkin Mutum Biyu dake karamar hukumar Gassol a jihar Taraba, ya jagoaranci zuwa makabarta domin halartar jana’izan iyalainsa da ‘yan ta’adda suka halaka bayan sunyi garkuwa da su.

A ranar 19/1/2023 ne dai masu garkuwa da mutane suka kutsa cikin gidan Sarkin garin na Mutum-biyu sukayi garkuwa da matansa biyu da yaran sa su biyar.

Inda suka nemi fansar naira miliyan dari da sittin daga wajan mahaifinsu, amma basu samu ba. Shine suka yi musu kisan gilla ta hanyar daukar fansar hanasu kudi da akayi.

Tuni dai rundunar jami’an tsaron jihar taraba sun bayyana cewa zasuyi kokarin su, domin ganowa gaskiya akan wannan lamari daya faru da sarkin tare da iyalan shi, dama sauran al’umma baki daya.

Sun bayyana hakane yayin halartar wurin gudanar da sallar jana’izar ‘ya’yan basarake yayin da sukaji al’umma sunata allah wadai dangane da wannan rashin adalcin na ‘yan bindigar akan kisan ‘ya’yan basarake.

Kuci gaba da kasancewa da shafin ku mai albarka Janzakitv, domin samun ingantattun labarai na gida dana waje dama duniya baki daya mungode masoya

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *