May 18, 2024

An Gudanar Da Sallar Jana’izar Aisha Maina Wacce Ta Rasu Bayan Awanni Shida Da Yin Posting A Shafukan Ta Na Sada Zumunta kamar irin su Facebook, Twitter, Telegram, WhatsApp, da sauran su.

Anyi Mata Sallar Jana’izar ne a birnin jihar Sokoto inda ɗaruruwan mutane suka halarta kamar yadda addinin musulunci ya koyar ayiwa dukkan mamaci idan ya rasu.

Kafin rasuwar Aisha Maina tana rike da mukamin mai baiwa Gwamna jihar Sokoto shawara na yau da kullum domin ganin ansamawa al’ummar jihar farin ciki a zukatan su.

Hakika wannan mutuwa ta hajiya Aisha Maina al’ummar jihar sokoto bazasu taba mantawa da ita ba kwana kusa musamman talakawan jihar ta sokoto domin suna matukar samun farin ciki daga gareta.

Bugu da kari Marigayiya Aisha Maina: ta kasance itace wacce tayi fice wurin baiwa gwamnan jihar na sokoto shawara dangane da yadda za’a inganta rayuwar talakawan jihar ta sokoto.

Daga karshe muna mika sakon ta’aziyya ga ‘yan uwan marigayiyar Aisha Maina allah ubangiji yayi mata rahama tare damu da iyayen mu, baki daya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *