May 14, 2024

YANZU-YANZU: Yan bindiga sun kai hari wani masallaci a Zamfara, sun sace Masallata..

A ranar Juma’a ne wasu ‘yan bindiga suka yi garkuwa da wasu masu ibada a wani masallacin Juma’a da ke unguwar Zugu a karamar hukumar Gummi ta jihar Zamfara…

A ranar Juma’a ne wasu ‘yan bindiga suka yi awon gaba da wasu masu ibada a wani masallacin Juma’a da ke unguwar Zugu a karamar hukumar Gummi ta jihar Zamfara.

Mazauna yankin sun ce ‘yan bindigar sun boye bindigunsu a cikin tufafin su, inda suka kutsa cikin masallacin a lokacin da Limamin zai fara gabatar da huduba.

An ce masu kutsen sun ce wadanda ke wajen masallacin su shiga ciki.

“Lokacin da suka yi wa masallacin kawanya, sai suka bukaci wadanda ke wajen da su shiga cikin masallacin, suka shaida wa masu ibada cewa, sun zo ne domin tattaunawa a sako wasu da aka kama masu.

Ba wanda ya gan su da bindigogi kuma mutane da yawa sun zaci cewar su masu ibada.

Babu wanda ya kula su domin sun boye bindigogi, sai dai jim kadan da shigewa cikin masallacin sai suka fito da bindigu tare da yin harbin gargadi.

Sun garzaya da jama’ar cikin daji amma wasu daga cikin masallatan sun yi nasarar fita daga masallacin domin tsira da rayukansu.

Limamin na cikin wadanda aka yi garkuwa da shi amma Ladanin ya samu nasarar tserewa daga harin.

An kuma sace wasu da suke wajen masallacin saboda ba su san cewa wasu ‘yan bindiga sun kewaye masallacin ta waje ba.

Sun yi harbin bindiga da dama sama sannan suka koma daji tare da wadanda suka yi garkuwa da su.

Kakakin rundunar yan sanda ya ce bai san da faruwan abin ba amma za su binka.

Allah ya kawo mana tsaro da zaman lafiya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *