Jama’a Ku Taya Ni Da Addu’a, Ina Cikin Matsanancin Yanayi Na Rashin Lafiya, Cewar Jarumin Finafinan Hausa, Umar Yahaya Malumfashi (Bankaura) – Shiga ku ga yanda ya koma..

Janzakitv ta ruwaito daga majiya mai karfe cewa Tsohon ɗan wasan kwaikwayon nan Alhaji Umar Yahaya Malumfashi (Bankaura).

Ya bayyana cewa ya na buƙatar addu’a daga al’ummar Annabi saboda yanayin rashin lafiyar da ya ke ciki, wanda ya kai har an kwantar da shi tsawon lokaci a wani asibiti a Kano.

Bankaura, wanda a yanzu ake kira Yakubu Ka-Fi-Gwamna saboda rol ɗin sa a diramar ‘Kwana Casa’in’ ta gidan talbijin na Arewa24.

Ya na daga cikin daɗaɗɗun ‘yan wasan kwaikwayo da Arewa ke ji da su, domin ya fara dirama ne tun kafin a assasa masana’antar shirya finafinai ta Kannywood.

Lokacin da wakilin mujallar Fim ya samu labarin rashin lafiyar, ya garzaya gidan sa da ke unguwar Hotoro Tsamiyar Boka a ranar Litinin, 19 ga Satumba, 2022
Daga can aka tura shi wani asibitin kuɗi mai suna Pinnacle Special Hospital da ke unguwar Hausawa kusa da Masallacin Murtala inda ya same shi a kwance magashiyan.

Wakilin mu ya ruwaito cewa da ƙyar ya gane ɗan wasan saboda yadda rashin lafiyar ya ci ƙarfin sa, ya zama kamar ba shi ba.

Daga kwance a gadon sa na jinya, Bankaura ya faɗa wa wannan mujallar cewa: “Ka zo lokacin da ba zan samu damar da zan iya doguwar magana da kai ba saboda yadda na ke a yanzu, amma na gode da zuwan ka waje na.”

Duk da haka, ya ɗan yi bayanin cewa: “Na samu lokaci mai tsawo ba ni da lafiya, domin tun a watan Ƙaramar Sallah na ke cikin rashin lafiyar.

“Kuma dai ka ga a yadda ka same ni. Kuma ina fatan ku ci gaba da yi mani addu’a; Allah shi ya san yadda zai yi da bayin sa.”

Haƙiƙa duk wanda ya san Bankaura, idan ya gan shi sai ya tausaya masa, domin ya na cikin yanayi na buƙatar taimako.
Allah ya ba shi lafiya, ya sa cutar ta zama kaffara a gare shi, amin

Leave a Comment