June 22, 2024

Jarumar Masana’antar shirya fina-finai da ke arewacin Najeriya Jamila Nagudu, ta shaida cewa a Yanzu babu abinda tafi muradi sama da Aure.

Jamila Nagudu ta bayyana hakan ne a wata tattaunawa da tayi da sashen Hausa na radio Faransa. Ta ce ta shafe sama da shekaru goma tana taka rawar gani a masana’antar, to dole na nemi canji da yafi na irin yanayin da take ciki.

ta ce a baya suna iya fita aiki sama da sau goma ko wanne wata, annan yanzu da harkar ta ja baya bai wuce a wata su fita aiki sau biyu zuwa uku ba. Nagudu ta ce duk duniya babu harkar da tafi mata harkar fim, domin juya ita ta iya. Kana tana fata idan ɗanta yana da sha’awa ya tsunduma ciki.

Nagudu Ta Bayyana Manyan Kalubalensu
Da aka tambayeta ko wanne kalubale suke fuskanta? Nagudu ta ce kalubalen bai wuce yadda suke fuskantar barazana daga masu fassara fina-finan India zuwa Hausa ba, domin a cewarta hakan ya sanya sun samu koma baya sosai.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *