May 18, 2024

Kamar yadda kuka sani Adam a zango jarumi a masana’antar kannywood inda wasu lokutan yake rera wakoki tare da hawa mamin din su, a wannan lokacin ne jarumin ya bayyanawa duniya abin da yabata masa suna.

A shirar da jarumi Adam a zango yayi da gidan jaridar BBC HAUSA, a cikin wannan shirin nasu na daga bakin mai ita wanda dama sun jima suna wannan shirar da jaruman kannyood ko ‘yan siyasa da dai sauran su.

Jarumi Adam a zango ya bayyana abubuwan da suka shafi rayuwar sa kama daga harkar sana’ar sa ta fim wanda yake gudanarwa har ma abin da bai shafe ta ba.

Sannan kuma ya bayyana abubuwan da suka faranta masa rai, inda ya bayyana dan sa na farko a matsayin wanda yake faranta masa rai sosai wanda har ma yasawa dan nasa sunan abokin sana’ar sa wato Ali nuhu.

A cikin bidiyon shirrar da Adam a zango yayi da BBC HAUSA zakuji yadda ya bayyana abin da yabata masa suna a rayuwwar sa, wanda tun farkon rayuwar sa har kawo yanzu babu wani abu da yabata masa suna kamar wannan abin da aka masa.

Ga wadanda babu sani jarumi Adam a zango shine mutum na farko wanda hukumar tace fina-finan hausa ta kannywood dake jihar Kano ta kama, sannan kuma ta aike da shi gidan gyaran hali karkashin shugabancin Abubakar Rabo a shekarar 2007.

An kama jarumi Adam a zango ne dalilin wani Album din waka da yasaki mai suna Bahaushiya, amma bayan wasu kwanaki jarumin ya fita daga gidan gyaran halin sakamakon daukaka kara da aka yi.

Wannan shine kadan daga cikin shirar da BBC HAUSA tayi da jarumin kannywood Adam a zango, inda zakuji cikekkiyar shirar tasu a cikin bidiyon da muka ajiye muku a kasa.

Ga bidiyon nan domin ku kalla.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *