June 12, 2024

Wa’yannan mawakan a yanzu haka suna chan kasar Maiduguri domin gudanar da wani wasa na murnar zagayowar ranar da aka bawa Nigeria yancin kai wanda ake gudanarwa a kowanne state a kasar nan domin nuna farin ciki.

Wannan Magana idan kuka kalleta haka take babu wa’yanda ake zagi a wannan garin kamar wa’yannan mawakan amma kuma abinda zai baku mamaki shine a duk lokacin da sukaje waje sai aga ana shaukin zuwansu wanda akeyi musu wani abu domin nuna farin ciki wanda ba kowanne mawaki akeyi ba a wannan kasa ta Nigeria.

Mr442 shine wanda ya jagoranci tawagarsa zuwa wannan garin saboda suyi wasa kuma su nuna farin cikinsu suma akan wannan rana inda wannan wajen ya cika tam da mutane mata da maza duka a yayin wannan wasan wanda an yaba masa da nishadantar da mutane ta hanyar yi show.

https://youtu.be/aOp6vanGjGU

Anga safara’u da sweet Malika duka a wannan wajen wanda sune ma suka karawa wannan wasan armashi ta hanyar yi rawa da kuma wasu wakoki wanda masoyansu suke so daga cikin wakokinsu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *