Kalli Abinda Rashin Yiwa Budurwa Auren Wuri Ya Jawo

KinyuwaBudurwar Da Ta Balaga Aure Da Huri Kalli Irin Hatsarin Da Zai Biyo Baya.

Idan muka kalli yanda kullum tarbiyyar society ɗin mu ke ƙara sukurkucewa duk da yanda wa’azi da nasiha da jan-hankali ya zama gidan kowa da akwai, tun daga cikin masallatai na khamsu salawati, gidajen Radio, social media, kasuwanni, wayoyin hannu da dai sauran hanyoyi da malamai ke isar da nasihohin. Sai nake ganin da zamu koma mu gwada furmular da Manzon Allah ya bayar kan tarbiyyar yara, da tayiwu (Astaghfirullah yaƙini gareni) mu samu mafita a nan.

Wato ina nufin ta hanyar komawa da kuma yin aiki da hadisin nan da duk wanda ya kai shekaruna, da na sama dani muka koya a islamiyyoyi, wanda daga baya ban san me ya faru ba yayi ɓatan dabo a makarantun islamiyyoyin.

Ina nufin hadisin nan da Manzon Allah (S) yake cewa “addibuu auladakum” ku ladabtar da ‘ya’yayanku, “ala thalathi khisalin” a bisa abubuwa uku, “hubbi nabiyyikum” SON ANNABINKU “wa hubbi ahali baitihi” DA SON IYALAN GIDANSHI, “wa ƙira’atil Qur’ani” DA KARATUN AL’ƘUR’ANI

Domin ita fa soyayya ta gaske, tana haɗe ne da biyayya, matuƙar yara suka sha soyayyar Shugaba (S) da iyalan gidansa, to tabbas zasu taso da kwaikwayon ayyukansu.


Maimakon muhimmantar da musabaƙa da ƙaƙale wajen karatun Alkur’ani (wanda shi ma wannan ɗin yana da kyau a mataki na

uku kamar yanda ya zo a hadisin), to muke fara gabatarwa da yara ‘yan makaranta sanin ma’anonin ayoyin da suka zo kan yiwa Manzon Allah soyayya ta gaske kamar ayoyin:

Leave a Comment