Kalli Illar Kinyiwa Budurwar Da Tagirma ta Balaga Aure Da Huri

Kalli Illar Kinyiwa Budurwar Da Tagirma ta Balaga Aure Da Huri
HANKALI DA SAMARIN SHAHO YAN MATA

Yaudarar maza yanzu tafi yawa “wasu” sau tari namiji ya sani ba aure zaiyi ba haka nan bashi da niyyar yin aure amma sabod san zuciya sai yayi ta yaudar/lalata ya’yan mutane wasu ma daga cikin mazan har alfahari suke yi sbd yawan yan matan da suka lalata, kuma abun takaici kowacce idan suka je mata to suna zuwa da zancen aure amma da hakar su ta cimma ruwa to zaa neme su a rasa!!!
Sun gudu sai kuma suje wajan wasu Yan matan,irin wadannan samarin shahon sun kware wajan iya daukar hankalin mace da mayaudaran kalaman su wanda iyakar bakin sune yake tsayawa.

Sun kware wajan saka mace ta mace akan kaunar su,sai sunci galba a kan ta,daganan kuma sai a neme su a rasa sun gudu.

irin wannan lokacin ne za’a ga budurwa tana kuka sosai idan aka tsaurara bincike bawai iya kukan gudunwar tasa take ba aa akwai wani boyayyen Al’amari daya faru tsakanin su, shiyasa duk wadda aka yaudara indai har tasan bata bada kanta ba to Alhmdulillah komai yazo da sauki tayi wa Allah godiya shi kuma yaje can ya karata da yaudaran sa domin sai Allah ya Miki sakayya.

★Ana yawan fadawa maza wannan kalmar #KOMAI NAMIJI YAYI ADONE??? wannan kalmar tama da ina rudar masu wannan halin sbd sam ba abin ado bane,sbd idan ka lalata yar wasu zai zame maka mugun Ado daga lokacin da’aka fara lalata naka ya’yan ko kuma wataran aka wayi gari matar ka tana cin Amanar ka, duk wadannan abubuwan basu da dadi,, idan kace bazaa gani Ajikin kaba to ai baa yiwa Allah wayo dolen kane ka gani Ajikin zuri’arka idan ma baka gani ba zaa ganema, shidama wannan ai bashine ko baka biya ba zaa biyama babu ko sisi👌

★SAURAYIN RAGE DARE, wasu da yawa irin wannan sunan ake fada musu sbd abin nasu ya wuce lissafi yau suna wajen waccan gobe waccan!,,,,,,,
Basu da tsayayyar budurwa daya,zasu tsara mace fiye da tunanin ta yadda zata na zaton ita kadai ce a cikin zuciyar sa,irin wadannan samarin wasu har kudin aure suke kawo wa,amma idan bukatar su ta biya su tafi daman abinda sukayi niyya kenan.

Wani ma idan suka tashi yaudarar sai suce an musu mata A gida Alhali karyane kawai hakarsu tagama cimma ruwane sun samu Abinda suke so,wani kuma ma bazai gaya miki ba sai dai ki neme sa ki rasa,Yan mata ku kula wajan rike mutuncin ku fa.

Leave a Comment