June 10, 2024

Kalli Yadda Tsohuwa mai shekara tamanin da daya ta sauke alkurani


Kalli Yadda Tsohuwa mai shekara tamanin da daya ta sauke alkurani.

Dattijuwa mai suna Hajiya Asma’u Jibril wacce daliba ce a makarantar Hajiya Baraka Islamiyya Bachirawa a karamar hukumar Ungogo da ke jihar Kano, ta kasance daya daga cikin daliban makarantar sha biyu da suka yi saukar Kur’ani a karshen makon nan.
A hirarta da wakilin mu, Hajiya Asma’u ta bayyana kadan daga cikin abubuwan da suka taimaka mata wajen samun wannan nasara ta sauke Al’Kur’ani mai girma.

Acewar Dattijuwar, tun tana karama ta taso da sha’awar ta samu ilimi, kasancewar mahaifinta Malami ne, wannan ya sa ta ju tana da sha’awar ta gaje shi mahaifin na ta

Kalli Yadda Tsohuwa mai shekara tamanin da daya ta sauke alkurani
Mai girma Magajin Malam, Hakimin Ungogo, Alhaji Abdulkadir Ahmad Chedi, ya sawa daliban albarka, ya muma shawarci daliban makarantar da su cigaba da karatun Kur’anin da sauran litattafan addini da kuma kokarin kamanta aiki da su.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *