May 20, 2024

Warning: sprintf(): Too few arguments in /home/hurvr/public_html/wp-content/themes/chromenews/lib/breadcrumb-trail/inc/breadcrumbs.php on line 253

Ko Kun San Cewa Ali Nuhu Yafi Dauda Kahutu Rarara Kuɗi Nesa Ba Kusa Ba A Masana’ar Kannywood Kalla Kuga Videon Domin Ganin Bambancin Dake Tsakanin Attajiran Biyu (2).

Ba wai ana azumi ne kaɗai don a daina ci da sha (azumin baki) ba, ko don a horar da mu da yunwa, a’a; dukkan gaɓɓanmu, harshe, ido, kunne, hannu… suna azumi.

Azumin harshe (magana) shi ne kamewa daga zantuka marasa ma’ana, ko na haramci; kamar ƙarya, ƙazafi, gulma da yasassan zance (mis. jayayya akan kwallo ko siyasa), sai dai zikiri da ambaton kyawawan kalmomi.

  • Azumin ido (gani) shi ne kiyayewa daga kalle-kallen haramun a zahiri (kallen ƴan mata a titi) ko a cikin wayoyinmu, shiga shafukan baɗala sa fitsara a cikin wayoyi.
  • Azumin kunne (ji) shi ne kiyaye sauraron haram, raye-raye da kaɗe-kaɗe, gulmace-gulmace, laɓewa da jin sautukan ‘yan mata (wanda ba ajnabiyya ba), sauraron zantuka marasa ma’ana da sauransu.
  • Azumin hannu (taɓawa) shi ne kiyaye taɓe-taɓe, ko sata, ko taɓa kayan wani ba tare da izininsa ba.
  • Azumin ƙafa (tafiya) shi ne kiyaye takawa zuwa wajen alfasha (saɓon Allah); sai dai wurin aiyuka na halal, masallaci ko wuraren tunatarwa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *