Kokarin Ciro Wayar Salula A Cikin Masai Ya Janyo Mutuwar Wa Da Kani A Kano

Yaya da Kani sun rasa rayukansu a lokacin da suke kokarin ciro wayar salulu da ta fada cikin Ramin Shadda (Masai) a kauyen Aku da ke cikin karamar hukumar Gaya a jihar Kano.

Lamarin wanda ya fara faruwa lokacin da wani mai suna Haruna Abdullahi dan shekara 30 a duniya ya shiga cikin Masan domin ciro wayar tasa da ta fada kodayake ya kasa fitowa domin kuwa ya makale, hakan ta sanya shi kururuwar neman dauki da tallafi domin ya samu ya fito.
Ganau sun tabbatar da cewa, a lokacin da Abdullahi ke kururwar neman dauki, cikin hanzari Yayansa mai suna Adamu Danjummai, (45) shi ma ya bi kanin nasa domin kokarin taimaka masa ya fito daga cikin Masai din sai dai shi ma ya makale ya kasa fitowa wanda hakan ya janyo dukkaninsu suka galabaita, sannan Kuma rai yayi halinshi.

Da ya ke tabbatar da faruwar lamarin, Jami’in watsa labarai na hukumar Kwana-kwana ta jihar Kano, Saminu Yusif Abdullahi, ya ce “mun sami kiran gaggawa a ofishinmu na Gaya da misalin karfe 7:15 na safe daga wani Ali Ahmad wanda ya sa muka garzaya wurin cikin gaggawa domin bada namj gudunmawar.”

Abdullahi ya tabbatar da cewa an fito da dukkan wadanda abin ya rutsa da su a sume kuma daga baya aka tabbatar sun mutu, yayin da tuni aka mika gawarwakin ga Hakimin Kauyen Aku Adamu Isyaku domin musu jana’iza da birnesu.

Leave a Comment