June 20, 2024

Mijina Ya Daina Cin Abincin Da Na Girka Tun Bayan Da Naihu, Saboda Yana Kyama Ta”

Janzakitv ta ruwaito daga Aliyu Adamu Tsiga.

Ya yi ƙorafin cewa ba zan iya haɗa abincinsa ba saboda ya yi iƙirarin ina yin abubuwa marasa kyau da ƙazanta kamar tsafta da kuma jaririn yana yawan yin fitsari, da tumbuɗi kuma ina yin amfani da bakina wajen cirema jaririn majinar da ke cikin hancin shi, kuma a dalilin haka ne yake so mu sami ƴar aikin gida.

Tun daga wannan lokacin, kusan watanni 2 kenan baya cin duk wani abu wanda ni ce nayi tunda daga abinci ko wani abun sha.

Don Allah ku bani shawara domin ban san taya zan ɓullo wa lamarin ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *