April 16, 2024

Ku dena haifar yaran da bazaku iya kula dasu ba” – Nafisat Abdullahi

Jarumar masana’antar kannywood wacce take sharafinta a shirin nan mai dogon zango na, LABARINA, wato Nafisa Abdullahi, wanda tauraruwar take haskakawa a cikin shirin na, LAVARINA.

A yanzu ne muka sami wani labarin akan jarumar inda ta goyi bayan wani matashin sarmayi da yake tsokaci akan Hausawa, a lokacin data wallafa hoton wata jarumar kasar India mai suna Difika.

Jaruma Nafisa Abdullahi ta wallafa wannan hoton na jarumar kasar India wato, Difika, a lokacin sa take bayyana murnar ta na zagayowar ranar haihuwar ta, amma hoton da jaruma Difika ta wallafa tsiraicin jikin ta ya bayyana.

Wanda hakan ya dauki hankulan jama’a duba da yadda tsiraicin jikin jarumar ya bayyana, daga nan kuma sukayi ta cece-kuce akan hoton.

Bayan jama’a sunyi ta cece-kuce akan wannan hoton da jaruma Difika ta wallafa, sai aka sami wani matashin saurayi wanda shi kuma ya goyi bayan jarumar inda yake cewa.

Ku Hausawa haka kuke idan mutum zai yi wani abu wanda zai sanya ku nishadi to sai yayi wani abu na jan hankali, idan kuma bazai yi irin haka ba to ai bai dace ya bada nishadin ba, kuma abin dana fuskanta mafi yawancin ku hausawa ku munafukai ne.

Bayan wannan matashin saurayin ya fadi tsokacin nasa akan abin da Hausawa suke, sai kuma jarumar Kannywood Nafisa Abdullahi martani da cewa.

Ai dama Hausawa sune asalin munafukai, kamar yadda shafin Hausa Midiya suka ruwaito.

 
A Wani Bangaren Kuma

Kunsan cewa Nafisa Abdullahi Ta Kashe Fimdin Labarina Kurmus Daga Yusuf Abacha

Bai kamata Nafesa Abdullahi ta fito tayi
magana ba bayan ta fice a shirin firm na
Labari na mai Dogon zango.

Dan jarida Yusuf Abacha mai bincike kan
abunda ya shafi fina-finan yayi sokaci kan Wannan lamarin ga kadan daga cikin Karin Haske

Labarin wani fim ne mai dogon zango da yayi suna matuka a Arewacin Najeriya wanda Kamfanin Saira Movies ke haska.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *