May 20, 2024

Warning: sprintf(): Too few arguments in /home/hurvr/public_html/wp-content/themes/chromenews/lib/breadcrumb-trail/inc/breadcrumbs.php on line 253

Masha Allah Bidiyon Yadda Wata Kyakkyawar Budurwa Take Rera Karatun Al’Qur’ani Mai Girma Cikin Salo Mai Ƙayatarwa

Mutane da yawa na samun matsala wajen haddar Alqur’ani, ta yadda za ka ga wani ya kasa haddar gaba-daya, wani kuma idan yayi sai ta dinga zubewa, to insha Allah a cikin wannan rubutun zanyi bayanin hanyoyi mafiya nagarta da indai ka bisu, to Qur’ani Zai tsaya a cikin kwakwalwarka har ka koma ga Allah.

Kuma ina so ku sani, duk wanda zai kashe maka jiki akan cewa ba zaka iya ba, to cutarka kawai zaiyi, duk ayyukan da suka ma yawa, duk shekarunka, duk yarintarka, zaka iya haddace shi kamar yadda kowa yake shi, abinda kawai ya rage maka shine kayi tsari mai kyau, wanda shi wannan tsarin ya kasu gida biyu:

Kuma ku sani, a duniyar nan kaf, babu wanda bazai iya haddace Alqur’ani ba, sai dai mutum idan bai so ba, domin kaf litattafan da Allah ya saukar, shi kaɗai ne Allah yace ya yassare shi, ta yadda za’a iya haddace karatunsa duka.

wajibi ne idan zakayi hadda kasan karfin ƙwaƙwalwarka, wato kasan adadin abinda zata iya haddacewa, sanin wannan, zai taimaka matuƙa wajen cimma nasara a lokacin da kake kokarin haddar Alqur’ani.

Kowa a cikinku yasan kanshi, yasan abinda kwakwalwarsa zata iya ɗauka, dan haka, ya kamata kowa ya san wannan.

2. IYAKANCE LOKACIN HADDAR, TA YADDA BABU WANI ABU DA ZAI HANA KA YIN TA A LOKACIN DA KA TSARA

Mutane da yawa basu da consistency, jajircewa da kuma tsayawa akan tsari, shiyasa bama iya kaiwa ga Abinda muke muradin samu. Shi kuma Alqur’ani duk lokacin da ka bar shi baka yi ba, to kumawa da baya zaiyi, sai ya zama kamar ma bakayi wajen ba.

Akwai abubuwan faɗa da yawa, amma dole zan takaita saboda kada rubutun yayi yawa sosai, sai dai kafin na rufe, akwai jan hankali guda ɗaya, amma kuyi min Azuri a yanxu, saboda total words da aka bani nayi rubutu a facebook sun kare, amma insha Allah a rubutu na gaba zanyi bayani dalla dalla.

Ku biyo ni rubutu na biyu

UWA GA AL’QUR’ANI

Ka koyi suratul fatiha da ƙira’an habz da kuma warash, saboda ko baka san cuta ba matuƙar ka iya suratul fatiha yadda ya dace, wallahi zakayi tawassali dashi kuma zaka samu waraka!

Manzon Allah (SAW) yace ka tsaya sosai ka koyi suratul fatiha fiye da dukkan surah a cikin Al’qur’ani, kuma yace idan da zaka haddace Al’qur’ani, amma baka iya suratul fatiha ba, to tabbas kana da buƙatan koyon hadda, kuma ya sake cewa idan har akwai inda yake baka wahala a karatun suratul fatiha, koda a sallah ne to ka riƙe AlQur’ani a hannunka yafi Alkhairi akan kayita sallah baka iya suratul fatiha ba. Tabbas da suratul fatiha ne ake karɓan sallah bayi, kuma itace uwa na Al’qur’ani, wanda ya kiyaye ta kuma yayi aiki da ita, wallahi ya samu shiriya, nikaina a matsayina na wanda ba kowa ba, wallahi nayi aiki da suratul fatiha sau berkete kuma Allah bai kunyata ni ba, ka koma ka koyi yadda ake karanta ta, kuma malamta baya sa mutum ya iya, haka ustazanta bayasa mutum ya iya, yadda ake koya hanya ɗayane tal shine kaje a koya maka, JazakAllahu khairan!

Bilal Omar Baba Gombe 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *