April 15, 2024

Masha Allah Ku Kalli Yadda Adam Zango Ake Nunawa Kyakkyawar Matar Sa Soyayya

ToMasha Allah Ku Kalli Yadda Adam Zango Ake Nunawa Kyakkyawar Matar Sa Soyayya
Biyo bayan wata bidiyo ta jan hankali da wata jaruma mai suna Nafisa Ishak ta wallafa a dandalin TikTok tana magana akan rashin dacewar rawa da kananan kaya da Mama Daso take yi a dandalin TikTok a daren jiya, jarumar ta bawa Mama Daso gakuri cikin tattausa lafazi

Tun bayan da jaruma Nafisa ta wallafa bidiyon jan hankalin ga Mama Daso take samin korafin rashin dacewa tayin data yi mata magana a matsayin wacce take sama da ita ko kuma muce ta haife ta, yayin da wasu kuma suke bata goyon baya.

Mun tuntubi Yakubun Producer mai kamfanin Gwammaja Intertaiment domin jin yadda al’amarin ya kasance har ta kai ga anyi sulhu, sannan kuma jaruma Nafisa ta fito ta bawa Mama Daso hakuri, kamar yadda zakugani a cikin biidyon.

An lakaɗawa maɗagwal dukan tsiya saboda rashin saka hannu ayiwa matarsa aiki.

“Shahararren ɗan wasan barkwancin nan mai suna Ali Artwok, wanda aka fi sani da Maɗagwal, ya sha dukan tashi kasha ruwa a Asibitin Barau Dikko da ke garin Kaduna, sakamakon ƙin sanya hannu a takardar shaidar fiɗa da za’a yi wa matarsa Hawa’u.”

“Matar nasa Hauw’u wadda ta shafe kwanaki uku ta na dogon naƙuda kuma likitoci sun tabbatar ba za ta iya haihuwa da kanta ba, bisani Maɗagwal ya ce shi yasan matarsa zata haihu da kanta in kuma ta mutu to shihada ta yi.

“Mahaifiyar Hauwa’u ta bayyana wa Jaridar Fasihiya baƙin cikinta da faruwar lamarin, domin har zuwa yanzu da Ƴar uwar Hauwa”u ta sa hannu kuma suka biya kuɗin aikin Maɗagwal ya ce bai yi nadama ba, kuma ba zai ƙyale duk wanda ya yanka masa mata ba.

Anyi nasarar ciro ɗa namiji zuwa yanzu. kuma za mu ci gaba da bibiyar lamarin kamar yadda rahoton hakan ke tabbatar mana da hakan.”

A Wani Bangaren Kuma

Waiwaye Akan Labarin Ummi Rahab
ABINDA YA RABA TSAKANINSU BA MAI KYAU BANE

Ance mahaifiyar Ummi Rahab itace ta damka amanar ‘yarta wa Adam Zango tun tana yarinya karama bata balaga ba

Kuma Adam Zango ya sakata a fina-finai har duniya ta santa, Ummi Rahab tana hannun Adam Zango har zuwa yanzu da ta balaga ta tumbatsa tana ganin ta kai
Gargadin Naziru Sarkin Waka Ga Masu Zagi

Mahaifiyar Ummi Rahab ta rasu watanni kadan da suka wuce, sai gashi yanzu an wayi gari Adam Zango ya sallami Ummi Rahab, ita kuma tana masa gargadi da ya dena mata batanci imba haka ba zata tona masa asiri

Kamar yadda aka saba Datti Assalafiy ya gudanar da bincike, kuma na samu tabbacin cewa tabbas Adam Zango ya rabu da Rahab, kuma rabuwar banza sukayi, rabuwar uwaka ubanka, na kuma samu bayani akan abinda ya rabasu har ita Rahab tayi barazanan tona masa asiri bayan BBC Hausa sunyi hira da Adam Zango a jiya Alhamis inda ya fadi wata kalma

Na fahimci cewa hakika mahaifiyar Ummi Rahab (Allah Ya jikanta) tayi babban kuskure da ta dauki amanar ‘yarta ta damkashi a hannun wanda shima yana bukatar a bashi tarbiyyah

Gaskiya wannan rayuwa rikon amana tayi karanci, cin amana ya yawaita, ba kowa ake bawa amana ba, wadanda ake ganin suna da tsoron Allah a wannan zamanin suna iya cin amana, balle ‘yan daudu masu lalata tarbiyyan al’ummah

Malaman tarbiyya Islama sunce, ko halal ce akwai wata halal din da ana barinta don kunya, balle abinda bai halalta ba

Shawaran da zan bamu shine:
Duk wanda Allah Ya bashi mata da ‘ya’ya musamman mata, to yayi kokarin basu tarbiyya ta addini, a wannan zamanin ba’a bada amanar mata, walau matarka na aure ko ‘yarka da ka haifa, idan suka samu tarbiyya da juriya suna sana’a ko mutuwa kayi zasu kubuta da taimakon Allah

Allah Ka tsare al’ummar Musulmin Kasar Hausa daga sharrin ‘yan Hausa film Amin Yaa Hayyu Yaa Qayyum

DAGA Datti Assalafiy

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *