Mawaki Rarara Ya Gwangwaje Ango Lukman da Amaryarsa Da Sabuwar Mota Shima DJ Ya Rabauta Da 50k..

Kwanaki biyu bayan kammala bikin Lukman na shirin Labarina, mawaki Rarara ya Gwangwaje ango da amaryarsa da sabuwar mota dal, wanda mutane ke nuna sambarka da lamarin da mawakin ya yi.

Kamar dai Yadda Aka sani a ranar Asabar din da ta gabata ne aka daura Auren fitaccen Jarumi a Masana’antar shirya Finafinan Hausa Yusuf Saseen Wanda Akafi Sani da Lukman Acikin Shiri me dogon zango Labarina.

A wurin Shagalin Bikin dinner ne aka hango fuskar mawaki Rarara inda yayi jawabi na minti biyu kamar yadda ya yi alkawari, domin tun kafin bikin ma yayi alkawarin cewa indai lokacin yayi to tabbas zai halarci wurin taron wanda hakan yasa ya cika alkawarin sa.

A lokacin da yake jawabi ne sai DJ ya saka wakar da Rararan yayiwa zababben dan takarar shugaban Kasar Nigeriaba Jam’iyyar APC watau Bola Ahmed Tinubu sannan kuma ya roki rarara daya bashi kyautar mota, amma dai hakan bata samu sai dai yace zai basu dubu hamsin hamsin shida MC.

A Kyautar da rararar yayiwa Ango da Amaryar sa kuwa ya bayyana cewa zasu karba ne ta hannun mataimakiyar sa wato Aisha Humaira wanda kuma ana kyautata zaton cewa mota ce ya basu.

Leave a Comment