June 17, 2024

Nafi jin mutuwar Nura Mustapha Waye fiye da ta iyayena cewar Hajara izzar so.

Banji mutuwar iyayena ba kaman yadda naji ta Nura Mustapha Waye ba kasancewar su banyi rayiwa da su ba, Haka kuma Soyayyar mu dashu tasyi nisa domin ta kaimu ga Maganar Aure.

 Wata budurwa kuma fitacciyar yar wasan kwaikwayo wadda take taka rawa a fim din izzar so wanda marigayi Nura Mustapha waye ke bada umarni a cikin shirin ta bayyana soyyayar ta ga mai bada umurnin.

Aisha Babandi wadda akafi dani da Hajara a izzar so mai fotowa a diyar matawalle Tayi wata hira a gidan Radio Freedom dake Kano inda take bayyana cewa tashaku da nura Mustapha Waye kafin rasuwar sa har maganar Aure ta shiga tsaknin su.


A cikin hira da akai da ita anji wajen sa take cewa Sun shaku dashi sosai kuma shiya taimakawa rayiwar ta har ta zama tai suna, Ta kara da cewa ita marainiya ce bata da uwa da Uba, ta taso ne wajen yayar mahaifiyar ta.

Mutuwar Nura ta kasance min mutuwar da bazan taba mantawa da ita ba a wannan duniya luma har ila yau bazan manta dashi ba domin dan halak ne matuka.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *