May 27, 2024

Nafisa Abdullahi ta kuma yin magana akan Iyayen da suke tura yaran su barace-barace

Tsohuwar jaruma a masana’antar finafinan Kannywood, Nafisa Abdullahi tayi kalamai masu kaushi akan mutanen dake sukar finafinan Kannywood.

Jaruma Nafisa Abdullahi tayi wani rubutu a kafar sada zumunta ta Twitter ida ta bayyana rashin jituwa n dadinta a game da masu cewa finafinai Hausa na lalata tarbiyyar yara.

Mutane da dama dai na ganin cewa finafinan Hausa na wannan zamanin na zama wani abin gurɓata tarbiyyar yara, musamman yadda ake nuna wasu abubuwan da suka ci karo da al’adar Hausawa.

Tun bayan da fitacciyar jarumar ta bayyana ra’ayin ta dangane da yadda mutane suke haihuwa gaba gadi ta kuma shawarce su da su rage haihuwar yaran da basu da ikon da zasu iya ciyar dasu da kuma daukar nauyin su, jarumar take ta faman shan suka a wajen mutane domin hakan suna ganin ya saba da fahimtar su.

Haka dai bayan ba’a gama dayan ba, jarumar ta cire tsoro tayi magana akan Almajiranci da iyaye suke tura yaran su ko kuma muce barace-barace da akeyi a gari.

A rubutun da jarumar tayi ta bayyana cewa ba yadda za a yi mutane su bar yaran su na kallon finanfinan Hollywood, Bollywood dana kudancin Nollywood, sannan su buɗe baki suce finafinan Hausa ne ke ɓata tarbiyya.

Ga kalaman da jarumar ta wallafa a shafin nata na twitter.

Kuna kallon finafinan Hollywood, finafinan Bollywood da finafinan turanci na Najeriya, sannan ku zo ku ce finafinan Hausa ke ɓata tarbiyya… haba? Kuna barin yaran ku su kalla, suna amfani da wayoyi da yanar gizo, amma…. finafinan Hausa ke lalata tarbiyya. Ba su da tarbiyya dama tun farko.

Nafisa Abdullahi ta kuma yin magana akan Iyayen da suke tura yaran su barace-barace

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *