June 19, 2024

Ficaccan mawaki Naziru M Ahmad ya saki wata bidiyon wakar sa da mata suke rawa suna juna duwaiwai

Kamar yadda kuka sani Naziru M Ahmad wanda kuka fi sani sa Sarkin waka ficaccan mawaki ne a masana’antar kannywood wanda yayu fice ta dalilin wakokin da gake rerawa manyam masu kudi da sarakuna da ‘yan siyasa.

Naziru M Ahmad wanda a yanzu yana daya daga cikin shahararrun jarumai a cikin shirin nan mai dogon zango wato LABARINA, wanda ya rera wakokin da suka kara daukaka shi a cikin shirin

Mawaki Naziru M Ahmad ya saki bidiyon wakar ne a shafin sa na sada zumunta Instagram inda a cikin bidiyon zakuga mata suna rawa suna bin wakar tasa.

Ga bidiyon nan domin ku kalla.

Matsalolin Da Ake Fuskanta A Gidan Gala

A ziyarar da wakilinmu ya kai zuwa gidan Dirama, idanunsa ya gane masa abubuwa daban-daban, sannan kunnensa ya jiye masa wasu daga ciki. Akwai abubuwan ban mamaki da ban tausayi gami da ban al’ajabi.

Abubuwan ban mamaki

Daga cikin abubuwan da ya gani na ban mamaki su ne, cin karo da cikakkiyar budurwa wacce da ka kalleta ba sai an yi maka bayani ba ka san gidansu akwai rufin asirin da ba rashi ne ko talauci ya kawo ta gidan ba, sannan kuma kuma za ka ga budurwar da idanka dube ta ka san ba rashin masoyi ne ya kawo ta wannan wuri ba, saboda irin kyan halittar da Allah ya yi mata.

Wata kuma za ka ganta ita ba kyau ba, bab

saboda irin kyan halittar da Allah ya yi mata.

Wata kuma za ka ganta ita ba kyau ba, babu cikakkiyar sutura sannan kuma ga kwarewa a tantiranci, domin a ganinta idan ba ta yi irin wannan zakewar ba kamar ba za ta samu kasuwa ba.

Abin Tausayi

Wani abin tausayi da zai iya sanya hawaye ko kuka shi ne, cin karo da yarinyar da bai kamata a ce an ganta airin wannan wuri ba, wannan ya hada kankantar shekaru, da kuma yunkurin ganin sai kwatanta abin da na gaba dai ta ke yi, mafi muni shi ne, wadanda suke da halayya ta neman mata, ko kuma mazinata su ne ke ta kokarin ganin sun kusance ta.

Za ka ga mutum wanda a haife ya yi jika da ita, amma ba shi da burin da ya wuce ya ga kusance da kwanciya.

Wakilinmu ya ce ya taba ganin yarinyar da duka-duka shekarunta ba su haura 12 zuwa 23 ba wacca saboda kankantarta ma in ban da aiken ta ba a bin da ake iya yi, amma wasu kuma kullum bukatarsu su ga sun kawar da ita.

Ba wannan ne ya bani mamaki ba, yadda a wasu lokutan za ka ga tana rike da karan taba sigari a hannunta tana zuka, hakan na nuni da ita ma ta fara hawa kan turba kenan.

Wani babban abin tausayi da ya gani a mazowa gidan domin aiwatar da sana’arsu shi ne, ganin masu manyan shekaru daga sashen wasu mata da har yanzu basu san Annabi ya faku ba a gidan suna zuwa kallon yadda yara matasa ke cashewa madadin su tub asu koma ga Allah.

Abin takaici da kaico

Wani abin da zai baka takaici kuma shi ne, Gidan Dirama ba gida ne da tsofaffin karuwai ke kwana ba, a a duk wacce ka gani in ma dai budurwa ce ta baro gidan iyayenta, ko kuma a a bazawara ce mai kuruciya da idan ba ta gaya maka ba ba za ka san sirrinta.

A halin yanzu mafi aksarinsu ba suna baro gida ne domin za a yi musu auren dole kamar a da can ba, a a suna fita ne domin sun fi karfin iyayensu su fada musu su ji, wasu ma suna fita ne da izinin iyayen domin su iyayen sun san ko da sun fada ba za su ji ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *