June 12, 2024

Ficaccan mawaki Naziru M Ahmad ya saki wata bidiyon wakar sa da mata suke rawa suna juna duwaiwaiKamar yadda kuka sani Naziru M Ahmad wanda kuka fi sani sa Sarkin waka ficaccan mawaki ne a masana’antar kannywood wanda yayu fice ta dalilin wakokin da gake rerawa manyam masu kudi da sarakuna da ‘yan siyasa. Naziru M Ahmad wanda a yanzu yana daya daga cikin shahararrun jarumai a cikin shirin nan mai dogon zango wato LABARINA, wanda ya rera wakokin da suka kara daukaka shi a cikin shirin. Haka kuma Sarkin waka ya sami karbuwa a wajan al’umma sabida kaunar sa da suke da kuma son wakokin sa, inda zakaga daga maza har mata suna sauraran wakokin nasa.Sai a yau kuma muka sani wata bidiyon mawaki Naziru M Ahmad wanda ya rera wata sabuwar waka wanda tayi dai-dai data gidan biki, inda a cikin bidiyon zakuga mata da yawa suna cashewa dalilin wannan wakar tasa. Mawaki Naziru M Ahmad ya saki bidiyon wakar ne a shafin sa na sada zumunta Instagram inda a cikin bidiyon zakuga mata suna rawa suna bin wakar tasa. Ga bidiyon nan domin ku kalla.Matsalolin Da Ake Fuskanta A Gidan GalaA ziyarar da wakilinmu ya kai zuwa gidan Dirama, idanunsa ya gane masa abubuwa daban-daban, sannan kunnensa ya jiye masa wasu daga ciki. Akwai abubuwan ban mamaki da ban tausayi gami da ban al’ajabi.Abubuwan ban mamakiDaga cikin abubuwan da ya gani na ban mamaki su ne, cin karo da cikakkiyar budurwa wacce da ka kalleta ba sai an yi maka bayani ba ka san gidansu akwai rufin asirin da ba rashi ne ko talauci ya kawo ta gidan ba, sannan kuma kuma za ka ga budurwar da idanka dube ta ka san ba rashin masoyi ne ya kawo ta wannan wuri ba, saboda irin kyan halittar da Allah ya yi mata.Wata kuma za ka ganta ita ba kyau ba, babu cikakkiyar sutura sannan kuma ga kwarewa a tantiranci, domin a ganinta idan ba ta yi irin wannan zakewar ba kamar ba za ta samu kasuwa ba.Abin TausayiWani abin tausayi da zai iya sanya hawaye ko kuka shi ne, cin karo da yarinyar da bai kamata a ce an ganta airin wannan wuri ba, wannan ya hada kankantar shekaru, da kuma yunkurin ganin sai kwatanta abin da na gaba dai ta ke yi, mafi muni shi ne, wadanda suke da halayya ta neman mata, ko kuma mazinata su ne ke ta kokarin ganin sun kusance ta.Za ka ga mutum wanda a haife ya yi jika da ita, amma ba shi da burin da ya wuce ya ga kusance da kwanciya.Wakilinmu ya ce ya taba ganin yarinyar da duka-duka shekarunta ba su haura 12 zuwa 23 ba wacca saboda kankantarta ma in ban da aiken ta ba a bin da ake iya yi, amma wasu kuma kullum bukatarsu su ga sun kawar da ita.Ba wannan ne ya bani mamaki ba, yadda a wasu lokutan za ka ga tana rike da karan taba sigari a hannunta tana zuka, hakan na nuni da ita ma ta fara hawa kan turba kenan.Wani babban abin tausayi da ya gani a mazowa gidan domin aiwatar da sana’arsu shi ne, ganin masu manyan shekaru daga sashen wasu mata da har yanzu basu san Annabi ya faku ba a gidan suna zuwa kallon yadda yara matasa ke cashewa madadin su tub asu koma ga Allah.Abin takaici da kaicoA halin yanzu mafi aksarinsu ba suna baro gida ne domin za a yi musu auren dole kamar a da can ba, a a suna fita ne domin sun fi karfin iyayensu su fada musu su ji, wasu ma suna fita ne da izinin iyayen domin su iyayen sun san ko da sun fada ba za su ji ba.Wakilimmu ya samu zantawa da wata uwar ‘ya’ya uku ‘yan mata biyu da namiji daya da ta nemi a sakaya sunanta, wadda daya daga cikin ‘ya’yan nata ta fita zuwa irin wannan gida na Dirama, inda ta bayyana masa cewa, ita ce ta bar yarinyar zuwa wannan gida.“Gaskiya ni ce nake barinta ta je don kai na, dalili kuwa shi ne, gara dai ko me za ta yi nasan tana dawo wa gida ai zan san halin da take ciki fiye da a ce ta fita ina fushi da ita, kuma ta ki dawowa gida.“Ka san yaron yanzu ka haife shi ne amma ba ka haifi halinsa ba, ai ina nan zaune take kawo min labarin wasu suna shafe shekara da shekaru ba su dawo gida ba. Ita dai ‘yar uwarta ka ga tana zuwa makaranta ta addini da ta Boko amma dai ita waccan mu nan muna ta addu’a Allah ya shirya mana, na yi kuka a farkon lamarin har na hakura sai dai‘yar uwarta ta ce ba ni hakuri, amma dai ban taba yi mata baki ba,”in ji ta.To ko yaya ‘yan uwan irin wadannan‘yan mata ke ji a ransu yayin da aka ce ‘yar uwarsu ta shiga irin wannan yanayi? Aminu wa ne ga ita wannan yarinya, ya bayyana wa wakilimmu irin halin da ya tsinci kansa lokacin da ya shigo ya samu mahaifiyarsu na kuka

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *