May 20, 2024

Nice jaruma ta farko da aka nema na taka rawa a fim din Labarina ba Nafisa ba cewar fati washa…

Nice jaruma ta farko da aka nema na taka rawa a fim din Labarina ba Nafisa ba cewar fati washa.

Fitacciyar jaruma a masana’antar kannywood fatima Abdullahi washa ta bayyana cewa itace jaruma ta farko da akai wa tayin fitowa a fim din labarina na kamfanin Aminu saira.

Shirin fim din labarina shiri ne da yay suna a masana’antar kannywood a cikin jerin fina finai masu dogon zango, kusan a iya cewa shine fim na biyu a cikin fina finai wanda suka karbu.

Labarina shiri me da kamfanin Saira movie suka fito dashi ake kuma haskashi a tashar Arewa24.

Jaruma Hadiza gabon ta tattauna da Fitacciyar jaruma a masana’antar fina finai wato fati wahsa a dandalin ta na kafar YouTube inda tai mata tambaya akan fim din labarina kasancewar ta chanji Nafisa Abdullahi a cikin shirin.

Wani abun ban mamaki shine da jarumar ta bayyana cewa ai dama tun farkon shirin ita akai wa tayin fitowa a matsayin sumayya ku kalli cikakkiyar hira a wannan Bidiyon dake kasa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *