May 18, 2024

Fitaccen Jarumi a Masana’antar Kannywood Sadiq Sani Sadiq Ya bayyana cewa shifa ba tarbiyya yazo koyarwa ba a Kannywood, kawai kudinsa yake nema, ya fadi hakanne a wata hira da akayi dashi a kafar yada labarai ta freedom radio kano.

Kamar dai yadda aka sani fitaccen Malamin Addinin Musuluncin nan Sheikh Idris Abdulazeez bauchi ya kalubalenci yan masana’antar shirya Finafinan Hausa akan cewa kaf dinsu babu me ilimin addini a cikinsu duk jahilaine

Wanda hakan ne ya tayar da cece kuce harma wasu daga cikin jaruman Kannywood suka maida masa Zazzafan martani akan maganarsa wanda daga cikin su akwai jarumi sadiq sani sadiq wanda ya bayyana cewa yana fatan ya mutu yaje ga Allah a matsayin dan Fim.

Sai dai Kuma daga baya yayi nadamar abinda ya furta hakan yasa yanzu ya bayyana cewa shifa dama ba Tarbiyya Yazo Koyarwa ba a Kannywood Kudin shi kawai yazo nema.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *