May 18, 2024

A cewar Daraktan Hisbah, Muhammad Sulyman, yaran sun hada da maza da mata, masu shekaru 14 zuwa 15, wadanda aka kama su da aikata laifuka daban-daban da ake zarginsu da yin illa ga rayuwarsu a matsayinsu na kanana wanda kuma abin kyama ne a addinin Musulunci.

Ya kara da cewa yara kananan sun amince da laifin da suka aikata don haka jami’an Hisbah suka yi musu nasiha kan illolin abin da aka kama su suna aikatawa, daga bisani kuma aka sako su zuwa ga iyayensu tare da yi musu gargadi da ka da su shiga irin wannan ta’asar da za a iya yin lalata da su da kuma zubar da tarbiyyar gidansu

Ya kuma gargadi sauran masu irin wannan niyya da a fadakar da su domin kuwa jami’an ba za su bar wani abu da zai bari a yi wa kananan yara fyade ba har ma da manya da ke yin dabi’u marasa kyau na shaye-shaye ko karuwanci.

FacebookTwitterEmailShare

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *