Qalu innalillahi yanzu yanzu faifan bidiyon murja ya fita mutane Qalu innalillahi yanzu yanzu faifan bidiyon murja ya fita mutane

Qalu innalillahi yanzu yanzu faifan bidiyon murja ya fita mutane

Ficacciyar Jarumar shirin nan mai dogon zango Izzar so wanda Tashar Bakori Tv dake kan manhajar Youtube take kawo muku a duk sati wato Aisha Najamu wacce a cikin shirin ake kiran ra da Hajiya Nafisa.

Ta bayyana a cikin wata bidiyo data wallafa a dandalin TikTok inda take kuka tana zubda hawaye wanda hakan abin a tausaya mata ne, inda take fadin cewa a ina aka taba ganin tana iskanci ko zina da za’a ce suna iskanci.

Hakan ya biyo baya ne lokacin da wani matashi ya yi musu kudin goro a dandalin TikTok, dama haka rayuwa take laifin da wani ya aikata sai kaga ya shafi wani amma abin da Aisha Najamu tayi yana nuna cewa ta fito ne domin ta wanke kan ta kan abin da ake zargin su da aikatawa.

A cikin bidiyon da zaku kalla zaku ga yadda Aisha Najamu take kuma tana fadin cewa, su sana’a suke amma ba ana kiran su da karuwai ba.

NAMIJI ‘DAN GOYO NE GA WADDA TA IYA!!!

Yake ‘yar’uwa musulma kisani cewa mijinki wani mutum ne mai daraja da kima da mutunci da ya kamata kisan girman shi,ki kuma bashi girman shi.wajibine kiyiwa mijinki biyayya ki rinka tausaya masa,ki rinka kula dashi ki rinka tattalinsa kamar kwai,ko ince kamar kudi.

Ance za’a iya cin nasaran mutum ta hanyar kyautatawa,kamar yadda ba’a iya cin nasaran mutum ta hanyar fitina.Da hali mai kyau, da kalma mai kyau,da siffa mai kyau,da abinci mai dadi,da kallo mai kyau,da tsafta na zuciya dana jiki dana kaya dana wuri,Hira mai dadi da sauran abubuwan kyautatawa,kamar yadda baza kici nasara ta hanyar komai ba.

Don haka ‘yar’uwa kisani cewa mijinki sitiyarin rayuwar sa gaba daya yana hannun ki,Don haka ke ya kamata kisan yadda zaki tarairaye shi,yadda zaki juyashi, yadda zaki lailaye shi ki kwantar masa da hankali.Ya zama cewa rayuwar shi ta gyaru ta hanyar ki, hankalinsa ya kwanta ta hanyar ki,rayuwarsa tayi kyau ta hanyar ki,shawarwarin ki da halayen ki masu kyau sun daidaita shi akan sahu madaidaici.

Wasu matan zaka gansu kazamai, gashi basu iya girki ba,in tayi miya kamar ruwan wanke kai,kuma mijin yana bata kudin cefanen amma saita cinye kudin taki yi ba.bata iya tarban miji ba,bata iya lallaba miji ba,bata san kalmomin soyayyar da yakamata ta rinka fadawa mijinta ba,ya dawo wurin aiki ya gaji ba abincin kirki ba hirar kirki dole kuwa ya kai dare a waje,saboda inya dawo gidan ba dadi,ko kuma kiyita zunbura fuska kina cin magani kina fushi,wallahi mata mu muke sanya maza su canza mana,domin inyaga takunki bana MACE TAGARI bace shima sai ya juye,ayita tafka rigima,gida ya zama kaman filin kaci uwaka.don haka QALUBALE GARE KU MATA.

Shiyasa sai kaga mata suna layin gidan bokaye suce sun kasa gane kan mijin,ya za’ayi kuwa ki gane kanshi,bayan kinki gyara kanki, idan har zaki yi waican abubuwan dana ambata a baya,to zaki sami soyayyar mijinki,zai soki zai kuma so ‘ya’yanki,Don haka mata ku gyara halayen ku,ku gyara zamanta kewarku da mazajen ku, kuma mazan kuji tsoron Allah ku gyara,ta yadda za’a sami gyara ta ko’ina.


Allah ya bawa masu iyali zaman lafiya,Allah ya basu ‘ya’ya mahaddatan, Al’qurani mai girma, Masu Taqwa,masu gaskiya,masu Amana,masu mutunci,wainda zasu kafa mana gwamnatin musulunci masu kuma yi adalici.Mu da ba muyi auren ba Allah ka bamu mazaje nagari,suma mazan Allah ka basu mata nagari Salihai. Wadda zamu yi zaman aure na gaskiya da Amana

Leave a Comment