May 16, 2024

Mafita Ta Samu: Sabuwar Sanarwa Daga Hukumar Npower Zuwa Ga Batch C Stream 2.

Assalam alaikum. Barkanku da zuwa wannan website na namu mai albarka, HausaTikTok .Com.Ng

Mun zo muku da wata sabuwar sanarwa daga Hukumar Npower game da posting na batch C Stream 2.

Hukumar tana mai kara ba wa al’umma hakuri game da jinkirin da aka samu a baya game da raba posting letter; PPA letter.

Idan ba ku manta ba a kwanakin baya Hukumar Npower ta fitar da wata sanarwa da ta nuna cewa Batch C Stream 2 za su karbi PPA letter su ne a Local Government, kuma sai aka akasin haka a wasu wuraran.

Akwai Jihohi da dama da suka fara raba posting letter, sai dai kuma an samu matsaloli da dama wajen rabon na PPA letter.

SABUWAR SANARWA DAGA NPOWER

A yanzu haka hukumar ta fitar da sabuwar sanarwa cewa kowa ya yi hakuri bisa jinkirin da aka samu na raba PPA letter. A yanzu haka State Focal Persons suna cikin aiki haikan wayan magance matsalar.

Sannan kuma da zarar komai ya daidaita za su dorawa kowa posting letter/PPA letter a dashboard dinsa.

Hukumar ta kara da cewa a yanzu haka babu wanda aka yi posting dinsa, duk wanda aka ba shi posting letter ko ya ga tasa a dashboard dinsa kwanakin baya an soke ta, da zarar komai ya daidaita za a dorawa kowa tasa. Mun gode.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *