June 20, 2024

Tunda Har Aka Tozarta Ni Ni Kuma Sai Na Ciga Ba Da Wakokin Batsa Ado Gwanja

Mawakin da yai kaurin suna wajen wakar iskanci kuma jarumi a masana’antar shirya fina finan Hausa ta Kannywood Ado Isa Gwanja ya bayya cewa, sakonsu yana ishewa fiye da na Malamai.

“Ana yarda da mu ana kallonmu, kuma ana sauraronmu fiye da yadda akewa Malamai, sabida a halin yanzu mutane sunfi karkata ga harkar nishadi fiye da jin wa’azi.”

Gwanja ya kara da cewar, haka Ilimin boko, Malamanmu na wancan lokaci da kuma mutanen kirki suka dinga kyamatarsa, aka bar harkar a matsayin kafirci, sai ya zamana mafi yawan wadanda suke Ilimin a wancan lokacin basu da llimin addini sai gashi a yanzu susuke mulkar al’umma.

“Haka ma maganar ‘Film Village’ maimakon a bari a yi shi a Kano inyaso sai a shigo da Malamai da Hisbah cikin lamarin gudun kar a dinga wani abu da bai dace ba, amma sai aka hana gabaday, to idan aka yi shi a wata jihar makociyar Kano fa? Kaga abinda ake gudu dole shi zai faru, maimakon a yi shi a kano a Musuluntar da shi kaga aka yi shi a Kaduna baza a Musuluntar da shi ba, kuma dole zai shafi yan Kano.” Inji Gwanja.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *