June 16, 2024

Warning: sprintf(): Too few arguments in /home/hurvr/public_html/wp-content/themes/chromenews/lib/breadcrumb-trail/inc/breadcrumbs.php on line 253

Idan Baku Manta Ba A Kwanakin Nan Ne Ake Tsaka Da Tattauna Labarin Wani Shirin Film Mai Suna ‘MAKARANTA’ Wanda Tashar Arewa Age Production Ta Dauki Nauyinsa.

Shirin Film Din Yazo Da Abubuwa Wadanda Ya Saba Al’adar Hausawa, Ta Wata Sigar Ma Musulunchi Bai Yadda Da Abubuwan Da Ake Bayyanawa Karara Ba Acikin Film Din.

Duk Da Ba Cikakken Bidiyon Film Dinne Ya Bayyana Ba, Tallarsace Kawai Ta Bayyana Amma Sai Dai Talla Tana Bayyana Abubuwan Da Shirin Film Din Ya Kunsa.

Biyo Bayan Bayyanar Tallar A Kafar Sada Zumuntar YouTube Sai Ake Gani Kamar Da Hadin Bakin Kungiyar Fina-finan Hausa Aka Shirya Wannan Film Din.

Sai Dai A Wata Hira Da Akayi Da Shugaban Hukumar Tace Fina-finai Isma’il Na’abba Afakallahu Ya Bayyana Cewa Bada Yardarsu Aka Shirya Wannan Film Ba, Hasalima Daraktan Shirin Ya Karya Musu Doka Tare Da Kin Yin Biyayya Kamar Yadda Hukumar Tace Fina-finai Ta Tsara.

Sannan Shugaban Hukumar Tace Fina-finai isma’il Na’abba Afakallahu Yace Har Yanzu Suna Kan Bincike Ga Lamarinnan Sannan Kuma Zasu Nemo Daraktan Shirin, Domin Su Yanke Masa Hukuncin Daya Dace.

Sai Dai Kuma A Wani Bangaren Daraktan Shirin Ya Bayyana Cewa Shi Baiyi Wani Laifi Ba, Haka Kuma Bazai Amsa Gayyatarsu Ba, Domin Hukuncin Hukumar Tace Fina-finai Yafi Karfine Akan Shirin Film Din Da Akayishi A Jihar Kano, Shi Kuma Ya Bayyana Cewa Ba’A Jihar Kano Ya Dauki Shirin Ba.

Sannan Ya Kara Da Cewa Shirin Film Dinsa Yana Dauke Da Abubuwa Masu Tarin Yawa Cikinsu Kuwa Har Da Kaciyar Mata Ga Dai Wata Bidiyo Dake Da Alaka Da Tirka-tirkar.

Zamu So Mu Karbi Ra’ayoyinku A Sashenmu An Tsokaci Akan Wannan Rohoto, Munaso Ku Danna Alamar Kararrawa Domin Samun Sababbin Shirye-shiryenmu Akoda Yaushe Mungode

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *