April 16, 2024

Shirin Jaruma Hadiza Gabon na Neman Hada Rigima Tsakanin Abdulamart da Mawaki Rarara.

Fitaccen mai bada umarni kuma babban darakta a masana’antar kannywood shugaban kamfanin Abnur Entertainment Abdul Amart Mai Kwashewa yayi bayani game da rayuwar sa da yadda ya samo sunan sa na Mai Kwashewa.

Daraktan da fari ya fara yiwa Dauda Kahutu Rarara raddi ne bayan da aka gayyace shi shirin Gabon Talk Show ya ke cewa ai Abdul Amart yaron sa ne, sai dai bayan gayyatar da akayiwa Abdul din ya bayyanawa duniya su ne suka fito da Mawaƙi Dauda Kahutu Rarara har aka sanshi a idon duniya.

Ya kara da fadin a baya Dauda Rarara din yana yin bidiyo ne tare da wasu wadanda bazamu iya ambatar sunan su anan ba,sai daga baya suka kawo mishi shiri na yadda abun zaiyi matukar daukar hankali da kuma jan ra’ayoyin duk dan wani jam’iya a Najeriya.

Kalli Cikakken vedion anan

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *