Tasirin mata makaranta Alkurani ya karu a duniya.

wani bincike da shashin Jaridar ATP Ingilishi yayi ya gano cewa yawan mata makaranta Alkurani a Najeriya ya nunku zuwa Rubi biyu, a shekarun baya maza da mata suna da kimanin mahaddata miliyan daya da dubu dari bakwai a fadin Najeriya. inda a halin yanzu a gano cikin shekarar 2022 zuwa 2023 mata sun ninka maza a yawan masu haddace Alkurani a makarantu, inda a gano cewa yawan mata masu haddace Alkurani sun kai miliyan biyu da Burbudi. Hakan ya Samo asali ne ta yadda Alummar Arewa musulmi su mayar da hankali wajen karatun Ya’ya mata a dukkan Sassan fadin Najeriya musamman karatun Alkurani a islamiyoyi.

Wani malamin islamiyya mai suna Malam saeed ya tabbatar wa Jaridar ATP cewa, galibin aji idan ka duba zaka ga Mata sunfi maza yawa a ciki. Haka duk shekara idan azo sauka ko yaye dalibai mata sunfi yawa. Wannan kadai zai nuna maka cewa Yawan karatun iyaye mata ya fi na maza da fifiko mai tarin yawa.

Leave a Comment