June 20, 2024

Tirkashi, Auren Wuri Maganin Zinar Wuri Bidiyon Yadda Aka Daura Auren Yaro Dan Shekara 15 ya Auri Yarinya Mai Shekaru 12 Yanzu…

Auren wuri maganin zinar wuri a nan wasu hotuna da ake yaɗawa a shafukan sada zumunta na cigaba da jawo muhawara inda ake cewa wani matashi ɗan kimanin shekaru 15 ya auri ƴar shekaru 12 yayin da wasu kuma ke cewa murnan kammala makaranta ce suke yi. APA dai bata tabbatar da sahihancin wannan labari ba.

A wani labarin kuma

Shugaban Ƙasar Ghana ya umarci a mayar da ɗaliban da aka kora makaranta sabo da sun zage shi

Shugaban Ghana Nana Akufo-Addo ya nemi Ma’aikatar Ilimi ta ƙasar ta sauya shawarar korar ɗaliban nan takwas daga makaranta sakamakon zagin sa da suka yi cikin wani bidiyo da ya karaɗe intanet.

Tuni ɗaliban suka nemi afuwar shugaban tare da neman ya nema musu gafara a wajen Ma’aikatar Ilimi kan ta janye hukuncin korar da ta ɗauka a kansu.

Wata sanrawa da Kakakin Ma’aikatar Ilimi Kwasi Kwarteng ya fitar a yau Juma’a ta ce Shugaba Addo ya shiga maganar bayan an faɗa masa abin da ke faruwa.

“Saboda haka, Ministan Ilimi Yaw Osei Adutwun ya umarci ma’aikatar ta ɗauki wani matakin na ladaftarwa a kansu a madadin kora,” in ji sanarwar.

Tun farko an dakatar da ɗaliban na makarantar sakandare ta Chiana Senior High School da ke Jihar Upper East kafin daga baya ma’aikatar Ghana Education Service (GES) ta kore su daga makarantar.

GES ta bayyana abin da ɗaliban suka yi da “abin ƙi kuma wanda ya saɓa da ɗabi’u na gari da aka san ɗalibai da su a Ghana,” a cewar rahoton shafin My JoyOnline.

BBC Hausa,

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *