May 18, 2024

Yanzu yanzu muke samun labarin yadda wata kotun shari’ar musulunci ta aika murja ibrahim kunya yar Tiktok, izuwa gidan gyaran hali.

Idan baku manta ba cikin wadannan kwanaki da suka gabane kungiyoyin manyan malamai dake jihar kano suka kai karar wannan yarinya da take bata tarbiyyan yaran mutane a shafinta na Tiktok wato Murja Ibrahim kunya.

Dukkan ma’abocin hawa shafin sada zumunta na Tictok, tabbas yasan wannan yarinya murja ibrahim kunya tana daya daga cikin masu bayyana kalaman da basu dace ba, musamman akan samari da ‘yan mata harda manyan mutane baki daya.

Sai ayau kotun shari’ar musulunci ta aikata izuwa gidan gyaran hali na tsawon mako biyu akan irin bayyana kalaman da basu dace ba, kuci gaba da kasancewa da Shafin Janzakitv, domin kawo muku cigaban labarin bada jimawa ba mungode

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *