June 17, 2024

Wannan jaruma kunsan babu wacce ta shigo kannywood da farin jini kuma har yanzu take kara samun cigaba kamar mome gombe saboda yanzu tabi sahun kananun jarumai wanda tauraruwarsu take haskaka kuma tana da kwazo gashi ta iya aiki sosai

Da farko ta fara aiki da mawaki Hamisu Breaker Wanda suke hawa wakoki tare kuma sun shaku da juna wanda wasu suke fada ma cewa ai mawakin auranta zaiyi an gama komai ashe duka jita jita ne abin babu wata maganar aure a tsakanin su.

Ta shigo kannywood tanada shekaru amma duk da haka tayi aiki kai kace bata wuce shekara ashirin ba amma kuma ana ganinta ansan ta haura haka kawai abinne a ranta shi yasa take iya bakin kokarinta domin yin abu daidai da wanda aka sakata da haka ta samu ɗaukaka har a kasar daba tataba

Babban abinda baku saniba game da wanan jarumar shine ta tabayin aure kafin ta shigo harkar kannywood wanda mutane da dama basu sani ba sai dai kuma bata taɓa haihuwa ba shi yasa babu wata alama da yake nuna cewa wannan jarumar ta taba aure domin ta kasance mace ceai kyau kuma gata doguwa gashi ta kware a harkar rawa.

Bugu da kari ba yar kano bace hasali ma gashi ajikin sunanta ta haɗa da sunan garin su hakan ya nuna cewa tana alfahari da garin da aka haife ta

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *