April 16, 2024

A wani lamari mai cike abin jimami da ya auku a jihar Kwara inda wani matashi ya halaka ƙanin sa yayin gwada maganin bindiga kamar yadda Jaridar Labarun Hausa ta rawaito.

Matashin mai suna Abubakar Abubakar ya harbi ƙanin sa har lahira mai suna Yusuf Abubakar ɗan shekara 12, domin gwada ingancin sabon maganin bindigan da suka siyo. Jaridar Daily Trust ta rahoto.

Mahaifin yaron matashi yana da bindigar farauta
Abubakar mamacin ƴaƴan wani mafarauci ne a ƙaramar hukumar Kaiama ta jihar Kwara.

An samo cewa lamarin ya auku ne a ranar Lahadi, sannan matashin Abubakar yayi ɓatan dabo tun bayan aukuwar lamarin. Ya gudu ne bayan ya aikata wannan ɗanyen aikin.

Hukumomi sun tabbatar da aukuwar lamarin
Da yake magana kan lamarin a ranar Litinin, kakakin hukumar ƴan sandan jihar Kwara, Okasanmi Ajayi, yace kwamishinan ƴan sandan jihar Paul Odama, ya bayar da umurnin a gudanar da bincike.

Ku Karanta Wannan: Za’a Kafa Hukumar Kula Da Magungunan Gargajiya A Kano

Bayan sun sha maganin bindigan, babban yaron matashi ya ɗauko bindigar farauta ta mahaifin sa sannan ya harbi ƙanin sa, maganin bai yi aiki ba wanda nan take matashi Yusuf ya rasu a wurin.

Okasanmi ya shawarci iyaye da su riƙa sa ido kan abubuwan da yaran su ke aikatawa.

Yakamata su dai na yin abubuwan da ba su dace ba domin hana aukuwar irin wannan lamarin a nan gaba, a cewar kakakin ƴan sandan.

Gajiyar tafiya ce, Martanin Fati Bararoji akan hotonta wanda aka ganta a komade
A safiyar jiya ne aka dinga yada wasu hotunan tsohuwar jarumar Kannywood, Fati Bararoji wacce tayi tashe a kwanakin baya a soshiyal midiya inda aka ganta duk ta komade, Fim Magazine ta ruwaito.

A yadda aka santa da cikarta da surarta, a hotunan duk an ga yadda ta zaizaye ta tsiyaye sannan tsufa ya fara bayyana karara a fuskarta, inda wasu su ka dinga zargin ciwo ne ya tasa ta gaba.

Sai dai Mujallar Fim ta nemi sanin karin bayani har wurin ita jarumar, inda aka zargi ta yi ciwon, ashe ba haka abin yake ba. An gano cewa jarumar ta wallafa hoton ne a status din TikTok dinta, wanda tun daga nan mutane da dama su ka dinga yadawa har da masu mata fatan samun lafiya akan cutar da ke damunta.

Yayin da Mujallar fim ta kirata a waya, ta bayyana cewa:
“Na yi mamakin yadda naji mutane na ta surutai kala-kala akan hotunana. Har da masu cewa ba ni da lafiya. To ni lafiya ta kalau kuma ban yi fama da wani ciwo ba.

“Na dai san na yi tafiya zuwa Abuja, daga can na wuce Sokoto don halartar wani biki, daga nan na dawo Kano.

“Yanayin tafiyar da kuma gajiya ne duk su ka sanya na fada, kuma sai na dauki hotunan da aka dinga zargin ba ni da lafiya. Gaskiya lafiyata kalau. Gajiyar tafiya ce kawai.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *