April 16, 2024

WATA SABUWA: Ku Gaya Min Dan Fim Daya Tak Mai Addini Tambayar Sheikh Imam Idris Abdul’aziz Bauchi.

Babban Malamin Musulunci dodon makiya Allah Sheikh Dr Idris Abdul-Aziz Bauchi ya jefa babban kalubale ga ‘yan film

Malam yace a nuna masa ‘dan film guda daya mai addini, indai dan film ne a nuna masa mutum daya mai addini yazo a masa interview, zamu tambayeshi menene addinin? Akwai addinin da babu bin shari’ah a cikinsa

Na ga wani wakilin ‘yan film ya fito yana mayar wa Malam raddi, har yana kokarin nuna cewa wai Malam yana da tabin hankali a kokarinsa na kare ‘yan film

Magana ta gaskiya duk mai addini idan ya tsaya ya kalli ‘yan film da kyau zai fahimci babu addini a tare da su

Shirya labarai na karya, da hada mata da maza rawa da waka baligai sanye da sutura irin na ‘yan iska wanda muke gani a tare da ‘yan film ba addini bane, kuma babu wanda zai shiga harkan ya kasance yana da addini

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *