Wawaye Ke Auren Soyayya Ni Dan Kudi Zanyi – Cewar Wata Sabuwar Amarya

Wata amarya mai suna Habiba Gado ta wallafa hotunanta a Facebook na kafin auren su ne tare da angonta wanda taken da ta yi wa hotunan ya yi matukar daukar hankulan mutane da dama.

Aure saboda kudi zan yi, babu abinda ya dame ni da shirmenku, a cewarta.

Ta kara da cewa “Wawaye ne ke auren soyayya.”

Ga wallafar tata:

Ba dai a tabbatar ko wasa take yi ba ko kuma da gaske take kuma har yanzu har yanzu bata bi bayan wallafar tara yi wata wallafar wacce za ta wanke waccan ba duk da fiye da mutane 2,000 sun yi ta tsokaci.

Shi kuma angon nata ya wallafa bidiyonsu tare na hotunan kafin aurensu inda shi ma yace, “Wawaye ne ke auren soyayya 2022.”

“Mutumin da ya samu mata ya samu abu mai tsada kuma Ubangiji ya yi masa babbar kyauta. Ni dai na samu tawa shi ne nace bari in sanar muku.”

Ga wallafar ta shi:

Rawar Tabara Da Mata Keyi A Yabo Yafi ta Tiktok
Fitacciyar mawakiyar finafinai a baya, yanzu haka kuma sha’ira a fannin yabon manzon Allah SAW, Maryam Fantimoti ta ce tabarar da mata sha’irai masu yabon ma’aiki su ke yi, ta fi ta ‘yan rawar TikTok da ‘yan fim.

Kamar yadda ta shaida wa Freedom Radio Kano, ta ce dangane da shigarsu ta fitar da surarsu, cakudewa tsakanin maza da mata da suke yi ya munana.

A cewarta:

“Abinda yasa nayi magana akan na hadarar manzon Allah SAW shi ne yadda ake yawan korafi akan yabon manzon Allah a gyara. Na daya a gyara alkaluma. Na biyu a gyara harshe, sannan a gyara dabi’a ta sha’irai.

“Saboda mu mata ne. Wata sha’irar idan ki ka kalleta sa’ar ‘yar da na haifa ce. Za ki samu ta yi shiga irin ta su ta yara.

“Ya kamata a gyara. Ina ganin kuma duk abinda ake yi yayin yabon manzon Allah SAW in dai ya saba wa dabi’a to ina tunanin wannan abin ya yi muni.”

A bangaren wata sha’irar ta ce sam ba haka bane. Bai dace a yi wa sha’irai kudin goro ba.

Batun shiga ce, yanayin waka da cakuduwa tsakanin maza da mata. Kuma hukumar tace finafinai tana iyakar kokarinta wurin tantance wakoki tare da tace su.

Ta ce yanzu haka dai an dena samun irin wadannan matsalolin.

mun samu labaran ne daga shafin

Leave a Comment