June 15, 2024

An kama wani kwarto yana tsaka da alfasha tare da tsohuwar budrwarsa a gidan aurenta bayan ya haka hanyar zuwa wurinta ta karkashin kasa.

Mijin matar ne ya kama tsohon saurayin bayan da ya tona hanyar shiga gidan ta karkashin kasa daga gidansa ba tare da sanin iyalansa ba.

Ana tuhumar mutumin ne da yunkurin yin kwartanci yayin da shiga gidan budurwarsa da aka kada shi a aurenta a gidan mijinta ta hanyar da ya haka a karkashin kasa.

Kasar Meziko ta shahara wajen gina hanyoyin karkashin kasa na sirri, wadanda masu safarar miyagun kwayoyin ke amfani da su don cimma burinsu.

Amma a wannan karon wanda aka kama ya yi amfani da hanyar ce don isa ga tsohuwar masoyiyarsa.

Mutumin mai sana’ar gini da ya fito daga garin Billas del Prado 1 da ke Meziko, ya dade yana hulda da matar wadda take aure a garin Tijuana kuma suke makwabtaka da tsohon saurayin.

Don tabbatar da cewa ba wanda ya gano ziyarar da zai kai wa masoyiyarsa mai suna Pamela, sai Antonio ya fara hakar wata hanyar karkashin kasa da za ta iya ba shi damar tafiya daga gidansa zuwa gidan su tsohuwar masoyiyarsa.

Antonio ya yi amfani da sana’arsa ta gini wajen gina wata tsukakkiyar hanya da za ta ba shi damar wuce wasu layuka ta karkashin kasa har zuwa gidan tsohuwar masoyiyar tasa.

Ya yi hakan da fatar idan ya kammala gina hanyar duk lokacin da yake bukatar ganin ta zai tafi gidan a sirrance, idan mijinta ya fita aiki.

Yadda asirin kwarton ya tonu

Yadda aka yi asirinsu ya tonu shi ne sun tsara lokacin da mijinta zai dawo gida, amma sai ya dawo kafin lokacin da ya saba.

Kwarton da matar suna tsakiyar masha’a a cikin gidan sai mijinta ya shigo.

Maginin ya yi yunkurin boyewa a karkashin gadonta don shiga hanyar da ya haka a kusa da gadon.

Rashin sa’ar da ya yi, mijin matar ya fara neman sa ko’ina a cikin gidan bai ga kwarton ba.

Daga bisani da ya leka karkashin gadonsu sai ya gano hanyar karkashin kasa da kwarton ya haka.

Da mijin matar ya bi ta cikin ramin da kwarton ya haka, sai ya bullo a gidan Antonio.

Kwarton ya yi ta rokonsa ya rufa masa asiri, saboda matarsa tana cikin wani dakin da yake gidan don bai son ta san abin da ke faruwa.

Hakan ya fusata mijin kwartuwar suka fara bai wa hammata iska a tsakaninsu.

Daga nan sai matar kwarton ta fito don ganin abin da ke faruwa na wani bako ya shigo cikin gidan mai gidanta yana bugun sa.

Hakan ya sa ta kira ’yan sanda, inda asirin mijinta ya tonu, ya bayyana laifin da ya aikata.

Kafafen sada zumunta na kasar Meziko sun yada labarin da hotuna, inda jaridun kasar da na kasashen waje suka yi ta wallafa rahoton.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *