May 23, 2024

Wata yarinya ‘yar shekara 14 ta bayyana wa kotu dake Ikeja jihar Legas yadda makwabcin mahaifinta Rafiu Sanusi ya rika yin lalata da ita dakin sa.

Yarinyar ta ce Sanusi wanda ta fi sani da Baba Aliyah ko Baba Maruwa ya fara yin lalata da ita ne tun tana shekara 12.

Ta ce Baba Maruwa kan yi lalata da ita ne a dakinsa a duk lokacin da ta kai wa mahaifinta ziyara a Amukoko.

Yarinyar ta ce wani Ibrahim ne ya kama Baba Maruwa yana lalata da ita ta window daga nan ya je ya sanar wa mafaifinta.

Mahaifina ya sanar da kakata abin da ke faruwa sannan ita kakata ta sa shi ya kai kara kotu.

“Ni Kuma aka kai ni ofishin ‘yan sanda da wani asibitin inda suka duba gaba na.

Mahaifin yarinyar ya ce tun bayan da matarsa ta rasu a shekarar 2017 ya kai ‘yarsa zama da mahaifiyarsa sannan lokaci-lokaci yarinyar na kawo masa ziyara a gidansa.

“Ashe duk lokacin da ta zo gida na sai makwabci na ya lallabeta da naira 10 ko 20 ya yi lalata da ita.

Sakamakon gwajin da aka gudanar a asibitin Mirabel Medical dake Ikeja ya nuna cewa an yi wa yarinyar fyade.

Alkalin kotun Ramon Oshodi ya ce za a ci gaba da shari’a ranar 27 ga Yuni.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *