Yadda Wata Matar Aure Ta Kama Mijinta Yana Cin Amanarta Ba Kunya Ba Tsoron Allah

Wata matar aure ta bayyanawa wata kotu dake kare hakkin da cin zarafin yara a jihar Lagos yadda mijinta ke bata maganin barci domin ya rika yin lalata da yar kanwarsa da take zaune a hannun mu tun tana yarinya.

Matar mai suna Aderemi Faleye ta ce mijinta Likita ne mai suna Femi Olaleye kuma yarinyar tun tana karama muke rikonta har ta girma duka a hannun mu.

Ta Kara da cewa minji nata ya dade yana yin lalata da yarinyar tun tana da shekaru 16 a duniya wanda Kuma yanzu ta cika shekara 18 da haihuwa.

Tace a kullum idan ya dawo yana bata magani Aspaspirin’ da ‘Phenergan wanda da Zarar tasha yana sa ta yi barci mai nauyin gaske ba tare da tasan me yake faruwa ba.

Idan tasha maganin tare suke kwanciya amma da zarar ya fahimci ta yi barci sai ya tashi ya nufi dakin da yarinyar take kwanciya ya yi lalata da ita.

Yarinyar ta fadawa Aderemi cewa Mijinta har ta dubura yake yin amfani da ita ba tare da jin tausayinta ba.

Sun shafe tsawon shekaru 11 da yin aure kuma suna da yaya biyu mace yar shekara 7 da namiji dan shekara 10, a cewar Aderemi.

Bayan da kotun ta saurari karar da ake yiwa Femi akan laifukan da ya aikata wanda ya hada da fyade, cin zarafi sai dai Femi ya musanta zargin wanda bayan hakan sai kotu ta bayar da belinsa.

Leave a Comment